1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

PDP na adawa da nadin Amina Zakari

Uwais Abubakar Idris GAT
January 4, 2019

A Najeriya babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta yi watsi da nadin Hajiya Amina Zakari a matsayin shugabar kwamitin tattara sakamakon zabe na kasa a bisa zargin kasancewa 'yar uwa ta jini ga Shugaba Muhammadu Buhari.

https://p.dw.com/p/3B2ma
Nigeria Präsidentschaftswahl 2015
Hoto: picture-alliance/dpa/Tife Owolabi

A Najeriya wata takadama ta kaure tsakanin hukumar zaben Najeriya da jam'iyyar adawa ta PDP a game da nada Hajiya Amina Zakari a matsayin shugababar kwamitin kula da tattara sakamakon zaben shugaban kasa da za’a yi a wata mai zuwa. Jam'iyyar ta PDP ta ce ba ta yarda da nadin nata ba. 


Sa'o'i kalilan ne dai bayan da Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Najeriya Farfesa Mahmoud Yakubu ya sanar da nada Hajiya Amina zakari a kan wannan mukami jam'iyyar adawar ta PDP ta fito karara ta ce ba ta yarda da wannan nadi ba tana mai zargin Hajiya Amina Zakari wacce dama ke a matsayin kwamishiniya a hukumar zaben Najeriyar da kasancewa mai dangantaka ta jini da Shugaba Muhammadu Buhari.


Tuni dai hukumar zaben Najeriyar ta mayar da martani a kan lamarin tana mai cewa a bisa dokar da ta kafa hukumar zaben Najeriyar dai, tana da iko da hurumi na nada jami’anta a kan aikin da take ganin suna da ikon aiwatarwa, abin da ya sanya ake mata kalon mai cikakken 'yanci. Bayanai dai sun tabbatar da cewa Hajiya Amina Zakari tsohuwar gwamnatin PDP ce ta nada ta kan wannan mukami kuma da ita aka yi zaben 2015. 

Nigeria Präsidentschaftswahl 2015
Hoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images


A yayin da hukumar zaben Najeriyar ke kara jadada cikakken shirinta na gudanar da zabe bisa gaskiya da adalci, da alamun da sauran kallo a kan wannan al’amari da ke sanya tayar da jijiyar wuya a dai dai lokacin da ake bukatar hadin kai, goyon baya da yardar kowane sashi a zaben na Najeriya da za a yi daga ranar 16 ga watan Febuwari mai zuwa.