1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel Papandreou

September 27, 2011

Jim kadan kafin kuri'a a majalisar dokokin Jamus, game da fadada shirin taimakon kudi ga kasar Girka, Pirayim ministan Giorgos Papandreou yazo nan Jamus, domin neman karin goyon baya daga Berlin.

https://p.dw.com/p/12hhu
Pirayim ministan Girka Giorgos Papandreou da shugabar gwamnatin Jamus Angela MerkelHoto: dapd

Yan kwanaki kalilan kafin a kada kuri'a a majalisar dokokin Jamus, game da fadada shirin taimakon kudi ga kasar Girka, Pirayim ministan kasar, Giorgious Papandreou yazo nan Jamus, inda ya halarci bikin ranar masana'antun Jamus, domin nunar da matsayi da bukatun kasar sa na samun karin goyon baya daga Berlin, game da gyare-gyaren da take gudanarwa. A lokacin wnanan ziyara, Pirayim ministan na Girka ya gana da shugaban gwamnatin Jamus, Angela Merkel.

A lokacin da yake jawabi gaban masu masana'antu da yan kasuwa a ranar masana'antun ta Jamus, Pirayim minista Giorgious Papandreou yace Girka tun daga yan watannin baya ta sami nasarori masu tarin yawa. To amma Girka inji shi, har yanzu tana bukatar karin taimako da goyon baya, musmman tana bukatar karin lokaci. Gyare-gyaren da kasar sa take gudanarwa suna da yawan gaske yadda shike ba za'a sa ran cikin dare daya za'a ga sakamakon su ba, inji Papandreou, inda ma yace babu kasar da tasan hakan fiye da Jamus., wadda bayan sake hadewar ta, ta sami canje-canje masu yawa.

Georgios Papandreou BDI
Papandreou: Taimako da goyon baya daga JamusHoto: dapd

Yace mun kaddamar da canje canje masu yawa a tsakanin yan watanni kalilan. Burin mu shine mu yi amfani da wannan hali na rikici da muka shiga a matsayin wata dama ta aiwatar da gyare-gyare. Ina tabbtar maku da cewar jarin ku a Girka ba zai maida mu baya ba, amma jarin zai zama sanadi ne na samun makoma mai haske ga kasar Girka.

Pirayim minista Papandreou yace Girka dai ba matalauciyar kasa bace, amma kasa ce da ba'a mulkin ta yadda ya dace. Duk da haka, yan kasuwa da masu masana'antun Jamus sun nunar a fili cewar batun zuba jari a kasar ta Girka baya cikin al'amuran dake gaban su a yanzu. Saboda haka ne idan ba tare da karin taimako karkashin shirin ceto na kasashen dake amfani da kudin Euro ba, kasar Girkan zata rasa kudaden tafiyar da aiyukan ta na yau da kullum.

Wannan gagarumin shiri na ceto kuwa za'a fara aiki dashi ne da zaran dukkanin kasashen dake rukunin masu amfani da Euro sun tabbatar da amincewar su. Samun wannan amincewa abu ne dake da matukar muhimmanci, inji shugaban gwamnatin Jamus, Angela Merkel:

Abin da yafi muhimmanci shine mu ga cewar Girka ta sami nasarar jan hankalin dukkanin kasashe ga matakan da take dauka. Mu Jamusawa zamu yi iyakacin kokarin mu domin tabbatar da hakan, zamu kuma yi iyakacin kokarin mu bisa ganin mun fita daga wannan mummunan hali, inda a maimakon ko wane wata a sami sabon mummunan labari, ya kasance mun kai yadda kasuwnanin mu zasu fahimci cewar Girka ta kama hanyar da ta dace.

Yan kasuwa da masu masana'antun Jamus suma dai sun baiyana fatan shirin na ceto da kasashen Turai suke niyyar gabatarwa za'a fadada shi, yadda Euro a matsayin kudin hadin gwiwa ba zai kasance cikin hadari ba. Hans Peter Keitel, shugaban kungiyar masu masana'antun Jamus yace a yanzu yana ganin kudin na Euro hadari.

Hans-Peter Keitel BDI
Hans-Peter Keitel, shugaban masu masana'antun JamusHoto: dapd

Kawo karshen hadin kan kudin Turai, zai haifar da mummunan illa ga Jamus da masana'antun kasar. Gaba dayan mu, muna sane da dangantakar dake akwai tsakanin masana'antun Jamus da kasashe Turai makwabtan mu. Duk wani abin da zai sanya ko wace kasa ta koma amfani da takardun kudin ta na asali ko kuma banbanta tsakanin kasashe masu amfani da kudin Euro, abu ne da zai kasance tattare da hadarori masu yawa, ba ma a fannin tattalin arzikiba amma har a bangaren siyasa.

Ranar Alhamis, idan aka zo kada kuri'u a majalisar dokokin Jamus gamea fadada shirin na ceto kudin Euro, masu sukan shirin ware Euro miliyoyi dubbai domin baiwa kasashen dake fama da matsaloli rance zasu kara daga muryoyin su. Dangane da haka ne Pirayim ministan na Girka ya nemi a mutunta kokarin da kasar sa take yi. Idan ba tare da hakan ba, al'ummar irin wadannan kasashe zasu rasa karfin zuciyar ci gaba da goyon bayan aiwatar da gyare-gyare a kasashen su.

Mawallafi: Umaru Aliyu

Edita: Usman Shehu Usman