Pistorius na neman karfafa huldar tsaro da Nijar
December 19, 2023Bayan ganawa da jakadan tarayyar Jamus a Jamhuriyar Nijar, ministan tsaron kasar ta Jamus Boris Pistorius ya gana da ministan tsaron Nijar Janar Salifou Mody a ofishinsa da ke birnin Yamai. Ministocin biyu sun sa labule inda suka tattauna ta tsawon awa daya da rabi kafin daga karshe su bayyana a gaban ‘yan jarida inda Kuma Ministan tsaron kasar ta Jamus ya yi bayani kan sakamakon da tattaunawar tasu ta bayar.
Pistorius ya ce: " Mun tattauna batutuwan da suka fi damun kowane daga cikinmu bayan sauyin mulkin da aka samu a Nijar. Abu mafi mahimmanci dai shi ne ta ya za mu ci gaba da aikin da muka kwashe shekaru muna yi tare a cikin nasara da mutunta juna a fannin taimaka wa al'umma. Na bayyana wa takwarana matsayar kasarmu kan Nijar, abin da ke yiwuwa a nan gaba a tsakaninmu da kuma wanda ba zai yiwu ba. Za mu tsara yadda huldarmu za ta kasance a nan gaba. Amma da sunan kasar Jamus, na sanar da shi bukatarmu sake maido da huldarmu, musamman ganin yadda ko bayan juyin mulki ba mu dakatar da ita baki daya ba."
Karin bayani: Nijar: Makomar sojojin Jamus a Sahel
Da yake bayar da amsa kan batun sake kulla hulda tsakanin kasashen biyu wato Jamus da nijar musamman a fannin tsaro, ministan tsaron Nijar Janar Salifou Mody ya ce kasarsa a shirye take ta dawo da huldar amma a bisa wasu sharudda.
Janar Maodi ya ce: " Mun fada cewa huldar tsaro da ta tanadi girke sojojin ketare a kasarmu a yanzu, mataki ne da ba za a dauka ba, sai an kiyaye dokokin da kasa ta tanada a wannan fanni. Ba za ta yiwu ba kawai wata kasa ta kwaso sojojinta da tankokin yaki ta zo ta girke a kasa ba tare da wasu sharudda ba. Don haka za mu zauna mu da mahukunta kasar Jamus mu tattauna sabbin sharudda da ka'idoji."
Neman farfado da aikin Jaamus na gina asibiti a Nijar
Wani batun na dabam da ministocin biyu suka tattauna shi ne na sake farfado da aikin gina katafaren asibitin sojoji da Jamus ke shirin yi a Nijar, amma aikin ya tsaya a sakamakon juyin mulki. Sai dai minitan tsaron Nijar Janar Salifou mody ya ce sun tattauna kan yiwuwar sake komawa aikin.
Karin bayani: Tallafin makamai ga Nijar daga Jamus da EU
Janar Modi ya ce: "Mun tattauna batun aikin gina babban asibitin sojoji wanda Jamus ta dauki nauyin ginawa a birnin Yamai. Lallai wannan aiki, an tsaida shi bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Yulin 2023. Amma ina kyautata zaton ba da jimawa ba za a koma ci gaba da wannan aiki."
A bisa jadawalin ziyarar ministan tsaron kasar ta Jamus zai ziyarci sojojin Jamus da ke girke a filin jirgin saman sojoji na birnin Yamai. Sai dai babu daya daga cikin ministocin da ya kawo zancen ko sojojin kasar ta Jamus za su ci gaba da zama a NIjar ko kuma za su fice ne daga cikinta kamar yadda sojojin Faransa suka yi.