1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Putin ya yi barazanar fito da sabbin makamai masu hatsari

July 28, 2024

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce akwai yiwuwar ya jibge manyan makamai a wurare na musamman domin tunkarar tunanin da Amurka ke da shi na jibge makamai masu linzami a Jamus.

https://p.dw.com/p/4ipwb
Hoto: Evgenia Novozhenina/REUTERS

 A yayin da yake magana a wurin wani faretin sojojin ruwa a Lahadin nan a  St Petersburg, Putin, ya ce ba za su zura wa Amurka ido ta aiwatar da sanarwar da ta yi a farkon watan nan cewa za ta jibge miyagun makamai a Jamus daga nan zuwa shekara ta 2026 ba.

Amurka dai ta kuduri aniyar jibge makaman ne a wani bangare na cikayarjejeniyartada kungiyar tsaro ta NATO da wasu kasashen Turai domin kara tsare kansu daga barazanar mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine a 2022. Sai dai Putin ya ce idan har Amurkan ta yi hakan, zai fitar da Rasha daga yarjejeniyar takaita amfani da wasu makamai da ta sanya hannu.

Sabuwar takaddamar tsakanin Rasha da Amurka dai ta dauko hanyar hassala kasashen karya dokar da suka rattaba hannu a kanta a shekarar 1987 da ta bukaci su daina amfani da wasu makamai da ke barazana ga wanzuwar dan Adam.