1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ra'ayoyin 'yan Najeriya kan gwamnatin APC

Muhamman Bello/ SBMay 26, 2016

Alummomin yankin Niger Delta sun shiga sahu wajen bayyana ra'ayoyinsu kan cika shekara guda cif da gwamnatin canji ta APC ta yi a Najeriya.

https://p.dw.com/p/1Iuk9
Nigeria Port Harcourt Arbeiter auf Plattform Ölförderung
Duk da cewa Najeriya na kan gaba wajen hako mai a Afirka amma kuma tana Fama da matsaloliHoto: Getty Images/AFP/P. Utomi Ekpei

A ranar 29 ga wannan watan da muke ciki na Mayu ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ke cika shekara guda kan gadon mulki. Gabannin zaben da dora kan iko dai, Buhari ya yi alkawarin daidaita al'amura a kasar ciki kuwa har da batun cin hanci da rashawa da ya lashi takobin ganin bayansa da kawar da matsalar makamashi da kuma rashin aikin yi.

Mutane da dama a sassan kasar ciki har da yankin Niger Delta na ta tofa albarkacin bakinsu dangane da cikar Buharin shekara daya kan mulki. Wani mai suna Mista Baridon Giadon ya fara da nashi tsokacin inda ya ke cewa "ni dai ga tunani na har yanzu babu wani abu a kasa domin akwai bukatar son ganin fuskokin 'yan Najeriya cikin walwala. Gwamnati ta ce ta cire tallafin man fetir, sannan ta sauya fasalin tafiyar da harkokin na man fetir kuma ni ban ga haka ba domin a sani na ba a kayyade farashi a sigar da sabon fasalin na harkokin man kasar ke gudana a yanzu ba."

Nigeria gefälschte Arzneimittel
'Yan kasuwa na kokawa da tarin matsaloli a NajeriyaHoto: Getty Images/AFP/P.U. Ekpei

Shi ma dai Mista Karigolo Ogolo daga yankin na Niger Delta a Tarayyar Najeriya ya yi nasa tsokacin kan shekara guda da mulkin ta gwamnatin APC a karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ya na mai cewa "bai yi wuri ba wajen auna kokarin wannan gwamnati ko akasin haka, amma dai a yanzu ana iya cewa tana kan aikin gina kasa, sai dai ba a kai inda ake so ba. Abin da zan iya cewa shi ne 'yan Najeriya na cike da takaici, 'yan Najeriya na da tsammani mai girma kan wannan gwamnati, don haka muke fatar cewa kafin ta cika shekaru hudu na mulki zamu ga sauyi."

Ita kuma wannan mata mai suna Ngozi Okaforna nata tsokacin ta yi kan wannan gwamnati ta Shugaba Muhammadu Buhari ta na mai cewa "shekara guda ta gwamnatin APC, gaskiya muna cikin yunwa, mun gaji, ba abinci, farashin kayayyaki sun tashi, gaskiya muna cikin damuwa, don haka gwamnati ta kara kokari."

Karikatur Buhari 1 Jahr im Amt
Zanen barkwanci kan irin ayyukan da ke jiran Shugaba Muhammadu Buhari na NajeriyaHoto: DW

Sai dai daga nasa bangare Mista Tony Kalogolo yaba kokarin da wannan gwamnati ta Shugaba Buhari ya yi ya na mai cewa "na san Buhari mutum ne mai mutunci da da'a, na iya tuna shirinsa na yaki da rashin da'a yayin mulkinsa na soji, kuma yanzu shi ne dai ya dawo, yanzu kuma da shirinsa na kawo canji, dan haka kada mu karaya, mu ba bashi dama, kuma mu duba yadda ake kwato kudaden sata daga barayin gwamnati, kudaden kuma da dama ya kamata a yi wa kasa aiki da su don amfanin ni da kai da ke da ku dan haka na aminta da cewa ya na akan hanya don gyara kasar mu."