Rabon zakka ya bar baya da kura a Najeriya
March 26, 2024Mutane hudu sun rasa ransu a jihar Bauchi ta yankin arewacin Najeriya bayan hatsaniya da ta barke tsakanin mata da jami'an yansanda wanda har ya kai ga yan sandan harba barkonon tsohuwa a wajen.
Faruwar haka baya rasa nasaba da mawuyacin yanayi na matsin rayuwa da al'ummar Najeriya take ciki da yasa adadin masu bukatar zakkar ya karu sosai, wanda ya saba da yadda a shekarun baya attajirin AYM Shafa ya saba fidda zakkar a kowane lokaci na watan azumin ramadan.
Bayanan da suka fito daga rundunar yansandan jihar Bauchi na mutuwar mutane hudu ta bakin kakakinta SP Ahmad Muhammad Wakil, sun sha banban da na wadanda suka kasance a wajen da hadarin ya faru.
Akwai bukatar sauya yadda ake ba wa mabukata tallafi a Najeriya
Salon hanyar da masu rabon zakkar suka bi a wannan gabar a jihar Bauchi wanda har ta kai ga samun mutuwar mabukata, na daga cikin silar da ake ganin ta zama abinda ya haifar da hadarin.
Masana kamar su Muhammad Mukhtar wani matashin malami a Bauchi ya bada shawarar cewa ana iya bude wa mabukata asusun ajiya a bankuna ko a shigar musu da tallafi ba tare da sun yi dafifi a wurin da ake bayan da shi ba, balantana ya haddasa turnitsitsi a wurin fidda zakkar.