1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahoton Amnesty kan kisan 'yan Shi'a

Yusuf BalaApril 22, 2016

Kungiyar ta ce cikin wadanda ta tattauna da su 92 ta ji cewa an kona wasu 'yan shi'ar da ransu.

https://p.dw.com/p/1Iae5
Amnesty international Logo
Hoto: picture-alliance/dpa/S.Kahnert

Kungiyar kare hakkin bil'Adama ta Amnesty International a ranar Juma'an nan ta bayyana cewa dakarun sojan Najeriya sun kashe daruruwan 'yan Shi'a maza da mata da kananan yara, bayan wata taho mu gama da dakarun sojan kasar da kungiyar 'yan Shi'a a watan Disambar bara, sai dai tuni dakarun sojan kasar sun yi watsi da rahoton kungiyar da suka bayyana da cewa kungiyar ta Amnesty ta dauki bayanai ne kawai na bangaren 'yan Shi'ar a cikin rahotonta.

Kungiyar ta Amnesty dai cikin rahoton ta ce dakarun sun kashe sama da 'yan Shi'a 350 ba bisa ka'ida ba a rikicin da aka yi a ranakun 12 zuwa 14 ga watan na Disamba. Har ila yau rahoton ya kuma nuna wasu hotunan tauraron dan Adam da ke nuna inda aka binne da yawa 'yan Shi'ar cikin wani katon kabari.

A binciken da kungiyar ta gudanar a watan Fabrairu na shekarar 2016, ta ce cikin wadanda ta tattauna da su 92 da suka ga yadda lamarin ya faru wani mai suna Yusuf ya fada wa kungiyar cewa da yawa daga cikin wadanda suka samu raunika da ba za su iya guduwa ba an banka musu wuta a raye.