1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane kusan 4000 suka mutu a rikicin makiyaya

Uwais Abubakar Idris
December 17, 2018

Kungiyar kare hakin jama’a ta Amnesty International ta fitar da wani rahoto a kan rigingimu tsakanin makiyaya da manoma da ta ce ya yi dalilin mutuwar kusan mutanen dubu hudu a cikin shekaru uku a Najeriya

https://p.dw.com/p/3AFxL
Nigeria - Gewalt zwischen Hirten und Bauern
Hoto: Imago/epd/A. Staeritz

A cewar kungiyar saboda dalilai na rashin hukunta masu laifi da daukan fansa a tsakanin bangarorin biyu, ya sa rikicin ya ta'azzara.

Mai shafuka 67, rahoton ya yi nazari mai zurfi a kan wannan matsala ta rikici tsakanin makiyaya da manoma da kungiyar ta Amnesty ta ce na daliin hallaka rayuwar mutane da dama fiye da na rikicin Boko Haram. Biyo bayan ziyara ta gani da ido a al'ummu hamsin da shida a jihohin Adamawa da Kaduna da Benue da Taraba da kuma Zamfara inda can matsalar tafi ta'azara.

Akwai dai wakilan bangarorin biyu da suka hallarci kaddamar da wannan rahoto wadanda dukkaninsu suka bayyana irin abubuwan da suka faru.