Rasha da Mali sun gamsu da sulhu kan Nijar
September 11, 2023Shugabannin biyu sun jaddada wannan matsaya ne a yayin tattaunawa ta wayar tarho da suka yi a ranar Lahadi (10.09.2023) kamar yadda fadar Kremlin ta Rasha ta sanar a cikin wata sanarwa da ta fitar.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da sojojin da suka kifar da gwamanati Mohamed Bazoum suka zargi Faransa da shirya kai wa Nijar hari ta yi amfani da wasu kasashen ECOWAS.
Karin bayani: Sojin Nijar: Faransa ta fara jibge makaman kai mana hari
A gefe guda kuma Shugaba Putin da Assimi Goita sun tattauna kan huldar Rasha da Mali a fannin tattalin arziki da kuma yaki da ta'addanci a daidain lokacin da kungiyoyi masu dauke da makamai da kuma 'yan tawayen Azawad suka fara tayar da kayar baya a Arewacin kasar biyo bayan fatali da yerjejeniyar Algiers.
Karin bayani: Mali za ta mutunta yarjejeniyar Algiers
Shugaban mulkin sojan na Mali ya kuma yi godiya ta musanman ga Rasha bisa goyoyn bayan ta ba wa Bamako a lokacin kuri'ar da aka kada a zaman kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kan bukatar ficewar dakarun MINUSMA daga kasar.