1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Sabon babin hulda da manyan kasashe

Gazali Abdou Tasawa
January 16, 2024

Shugaban gwamnatin Nijar Lamine Zeine ya jagoranci tawagar ministocinsa zuwa kasashen Rasha da Turkiya da Iran da kuma Sabiya a wani mataki na neman mafita ga takunkumin tattalin arziki na wasu kasashen duniya

https://p.dw.com/p/4bKIZ
Firaministan Nijar Ali Mahaman Lamine Zeine
Firaministan Nijar Ali Mahaman Lamine Zeine Hoto: DW

Tawagar ta Shugaban gwamnatin rikon kwaryar ta Nijar Malam Lamine Zeine wadda za ta kai ziyara kasashen Rasha daTurkiya da Iran da kuma Sabiya ta kunshi ministoci shida da suka hada da na tsaro da na man fetur da na noma da na kasuwanci. A hakumance dai gwamnatin kasar ba ta bayyana makasudin wannan ziyara ba, amma kuma tuni wasu masana suka soma hasashen cewa za ta rasa nasaba da kokarin samar wa kasar mafita daga takunkumin tattalin arziki da wasu kasashe suka kakaba mata ba. Wasu manazartan kuma na ganin batun huldar tsaro shi ne zai kasance a ajandar ziyarar tawagar.

Karin Bayani:Nijar za ta iya dakile takunkumin ECOWAS

Alhaji Yakouba Dan Maradi, shugaban babbar kungiyar ‘yan kasuwa masu shigo da kaya daga ketare ta SIEN ya ce akwai bukatar Nijar ta fadada huldarta da wadannan sabbin kasashe sai dai kuma dole za a koma hulda da abokanin huldarmu na gado idan komi ya daidaita.

Masu adawa da gwamnatin mulkin sojan na ganin kokarin bude sabon babbin hulda da kasashen Rasha da Iran da Turkkiyya da kuma Sabiya ba zai magance  matsalolin da Nijar ta shiga ba tun bayan juyin mulki.

Yanzu dai ‘yan kasar sun zura ido su ga sakamakon da wannan ziyara ta shugaban gwamnatin a wadannan kasashe wajen taimaka wa Nijar fita daga matsalolin da ta ke fuskanta a sakamakon takunkumin tattalin arzikin da kasashen duniya suka saka mata bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Yulin 2023