1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta bukaci Isra'ila ta tsagaita bude wuta a Gaza

October 12, 2023

Ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta bukaci Isra'ila da ta amince da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza domin samun damar shigar da kayan abinci da magunguna.

https://p.dw.com/p/4XTMN
Mataimakin ministan ma'aikatar harkokin wajen Rasha, Mikhail Bogdanov
Mataimakin ministan ma'aikatar harkokin wajen Rasha, Mikhail BogdanovHoto: picture-alliance/dpa/Sputnik/M. Blinov

Ma'aikatar ta ce, hare-haren da Isra'ilar ke kai wa a zirin Gaza na haifar da karuwar hasarar rayukan fararen hula. Mataimakin ministan ma'aikatar harkokin wajen, Mikhail Bogdanov ne ya bayyana hakan a lokacin da yake ganawa ta wayar tarho da babban sakataren kungiyar kwatar 'yancin kasar Falasdinawa wato OLP, Hussein Al-Sheikh. 

Karin bayani: Duniya na Allah wadai da sabon rikicin Hamas da Isra'ila

Isra'ila dai ta sha alwashin hana shige da fice a zirin na Gaza har sai an saki jama'arta da mayakan Hamas ke tsare da su, duk da irin kiraye-kirayen da ake mata kan ta amince a shigar da mai domin kula da marasa lafiya da suka cika asibitocin yankin.

Rashar ta kuma yin Allah wadai da rikicin da ta ce na salwantar da rayukan wadanda ba su ji ba su gani ba.