Rasha ta yi ikirarin kwace wani kauye na gabashin Ukraine
October 30, 2024Sojojin Rasha sun yi ikirarin kwace wani gari mai suna Krugliakivka mai mazauna 1200 da ke yankin Kharkiv na gabashin Ukraine. Wannan kauyen da ke da tazarar kilomita 20 kudu da Kupiansk, yana daga cikin wuraren da Moscow ta mamaye a tsakanin watan Fabrairu da Satumban 2022, kafin Ukraine ta 'yantar da shi bayan wani harin ba-zata.
Karin bayani: Ya Koriya ta Arewa za ta sauya yakin Ukraine?
Tuni dai, hukumomin Ukraine sun sanar da daura wa wasu karin mutane 160,000 damarar yaki, don ja wa Rasha birki. Sai dai sojojin Rasha na ci gaba da samun nasara a kan sojojin Ukraine sakamakon karancin dakaru da kuma jinkirin da kasashen yammacin duniya ke yi wajen samar musu da tallafin makamai. Cibiyar nazarin yaki ta Amurka (ISW) ta bayyana cewar dakarun Rasha sun samu gagarumar nasara a cikin wata guda tun bayan da suka sauya dabarun sojojin Ukraine.