Ukraine: Koriya ta Arewa za ta taimaki Rasha
October 25, 2024Ta ya ya taimakon Koriya ta Arewa ga Rasha zai shafi makomar yakin da take da Ukraine, kuma mai Kasashen Yamma ke yi domin dakile wannan manufa? Hadin gwiwa a fannin tsaro tsakanin Rasha da Koriya ta Arewa, ba wani sabon abu ba ne. Da ma dai a watan Yunin wannan shekara, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya je Pyongyang domin cimma matsaya kan kawancen tsaro da shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un. Sannan a baya, an yi ta rade-radi game da matakin Koriya ta Arewa, na bai wa Rasha makaman atilari. Kuma tun a farkon shekara ta 2023 Hukumar Leken Asiri ta Ukraine ta bayar da rahoton cewar, wata bataliyar sojojin Koriya ta Arewa ta isa yankunan kasar da Rasha ta mamaye.
Karin Bayani: Zargin musayar makamai tsakanin Putin da Kim Jong Un
Wani sakamakon binciken da Hukumar Leken Asirin Koriya ta Kudu NIS ta fitar ya nuna cewar, Pyongyang na son samar da sojoji dubu 12 domin taimakon Rasha a Ukraine. Tuni ma dai, ta riga ta tura dakaru 1,500 zuwa birnin Vladivostok mai tashar jiragen ruwa na Rasha. A halin yanzu NIS na magana game da sojoji 3,000 da aka riga aka tura Rasha, wadanda aka tanadar wa shigar burtu na Rasha don boye sahu. Amma har yanzu Rasha ko Koriya ta Arewa, ba su tabbatar da faruwar lamarin a hukumance ba. Sai dai Nico Lange babban jami'in a Cibiyar Tsaro ta Munich (MSC), ya ce babu kamshin gaskiya a wannan zargi.
Amma Ukraine na nuna damuwa game da karin goyon baya da Rasha ke samu daga kawayenta, saboda ana ganin shugaban kasar ta Ukraine Volodymyr Zelensky ya kasa samar da wani kwarin gwiwa daga Kasashen Yamma game da abin da ya kira "shirin nasara" a yakin Ukraine. Sannan kuma Ukraine na jin tsoron ka da Donald Trump ya lashe zaben shugaban Amurka a watan Nuwamban da ke tafe, saboda yana son katse taimakon makamai ga kasarsa. Trump dai, ya dora alhakin mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine a Zelensky cikin wani faifan bidiyo. Sai dai matakin Ukraine na neman taimakon kasashen yammacin duniya kan sabon kawancen Putin ba zai iya samun amsa kafin zaben Amurka na watan Nuwamban ba, a cewar Nico Lange babban jami'in a Cibiyar Tsaro ta Munich (MSC).
Karin Bayani: NATO za ta bai wa Ukraine karin makaman kakkabo jiragen yaki na sama
Mai magana da yawun kungiyar tsaro ta NATO a Brussels na cewar, idan sojojin Koriya ta Arewa suka shiga fagen yaki a Ukraine hakan na alamta haramcin goyon bayan da Pyongyang ke wa yakin Rasha da kuma kara nuna irin asarar sojoji da Moscow ta yi a fagen daga. A daya hannun kuma, kasancewar har yanzu kungiyar Tarayyar Turai ba ta mayar da martani kan zargin tura dakarun Koriya ta Arewa zuwa Rasha ba. Amma Roderich Kiesewetter masani kan manufofin ketare na babbar jam'iyyar adawa ta CDU a majalisar dokokin Jamus ta Bundestag ya ce akwai bukatar kasashen Turai su hada gwiwa wajen mayar da martani mai karfi ga Rasha, inda ya ce dole ne Jamus ta sauya kamun ludayinta ta hanyar kara mika makamai ga Ukraine.