Zirga-zirga tsakanin Nijar da Najeriya ta tsinke
September 1, 2023Talla
Yau kusan wata guda ke'nan da rufe iyakokin Nijar tsakanin kasar da makwabtanta ciki har da Tarayyar Najeriya biyo bayan matakin kungiyar ECOWAS na yin matsin lamba ga sabbin jagororin sojan kasar. Sai dai wannan mataki baya ga kassara mu'amalamar kasuwanci ya kawo tsaiko wajen sada zumunci tsakanin al'ummomin Najeriya da Nijar. Batun da shirin darasin rayuwa ya duba.