1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Rayuwar al'umma cikin garari

Uwais Abubakar Idris LMJ
March 29, 2022

'Yan bindigar daji sun tayar da wasu abubuwa masu fashewa a kan jirgin kasa da ya kwaso fasinjoji sama da 900, a kan hanyarsa daga Abuja fadar gwamnatin Najeriya zuwa Kaduna.

https://p.dw.com/p/49BeY
Najeriya I Kaddamar da Jirgin Kasa I Abuja I Kaduna
Rayukan al'umma na kara shiga cikin halin garari a NajeriyaHoto: DW/U. Musa

Harin dai ya yi sanadiyyar rasa rayuka tare da raunata mutane da dama, yayin da aka yi garkuwa da wasu fasinjojin da ke cikin jirgin kafin daga bisani jami'an tsaro su kai dauki a ceto sauran fasinjojin da ke cikin jirgin. Rahotani sun bayyana cewa 'yan bindigar dai sun dasa abubuwa masu fashewa ne a kan hanyar jirgin kasan, wanda bayan tarwatsa wani sashi na tarago ya tilasta masa ya kauce hanya a garin Rijana da ke kan hanayr zuwa Kaduna. Jim kadan bayan tarwatsewar abubuwa masu fashewar da suka tilastawa jirgin kauce hanyarsa, maharan sun kutsa kai ciki tare da yin harbin mai kan mai uwa da wabi. Daga bisani sun kuma kwashi mutane da dama.

Najeriya I Jirgin Kasa I Abuja I Kaduna I Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya MUhammadu Buhari tare da tawagarsaHoto: DW/U. Musa

Tuni dai gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da afkuwar lamarin, cikin wata sanarwa da kwamishinan kula da harkokin tsaro Samuel Aruwan ya sanyawa hannu. Sanarwar ta ce, an tura sojoji domin gadin jirgin. Hankula dai sun tashi musamman na 'yan uwan mutanen da ke cikin jirgin. Wannan dai, ba shi ne karon farko da 'yan bindigar dajin ke kai harin a kan jirgin kasan da ya zama hanayar da ta ragewa matafiya tsakanin Kaduna da Abujan ba. Koda a karshen mako sun kai hari kusa da filin jirgin sama na garin Kaduna, abin da ke nuna kara kaimi da ma zafafa hare-haren da suke yi a yankin Arewa maso Yammacin Najeriyar.