Yawan dauke wutar lantarki a Kamaru na dagula al'ammura
December 20, 2023Karar injin jeneretoya mamaye galibin manyan titunan birnin Douala cibiyar kasuwancin kasar Kamaru daya daga cikin manyan biranen kasar da suka fada cikin matsalar daukewar wutar lantarki babu kakkautawa inda wasu anguwanni ke shafe tsawon wini ko tsawon dare ba tare da samun wutar lantarki ba. Wannan daukewar wutar babu dare babu rana na tilasta wa duban 'yan kasuwa amfani da injin jenereto da duk karanci, da tsadar man fetur da kasar ke fuskanta 'yan kwanakin nan, tun da gwamnatin Paul Biya ta janye tallafin da ta sanya don rage wa al'umma radadin tsadarsa a watan Fabrairun wannan shekara.
Al'umma na cikin damuwa saboda rashin wutar lantarki
Ga ma ra'ayoyin wasu jama'ar: ''In muna amfani da jenereto, muna kashe kudi da yawa ga kuma farashin man fetur da ya haura gaskiyya muna cikin damuwa. Muna fuskantar matsala da kwastomomin saboda mun batar musu da lokaci ba za su iya hakurin jira ba masu neman sayen jenereto.'' A halin yanzu dai 'yan kasuwa na kokawa kan rashin sanin tabbas game da makomarsu sakamakon matsalar daukewar wutar lantarki da ake fuskanta musamman ma a wannan lokaci da mabiya addinin Kirista ke shirye-shiryen bukukuwan Kirismeti da karshen shekara.