1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Red Cross ta damu da kashe-kashen kananan yara a Gaza

November 7, 2023

Kungiyar Red Cross ta bukaci da a dauki mataki kan mace-macen yara kanana a rikicin da ke faruwa tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas a yankin falasdinawa inda ake luguden wuta.

https://p.dw.com/p/4YX6V
Jami'an agaji a Zirin Gaza
Jami'an agaji a Zirin GazaHoto: Ashraf Amra/AA/picture alliance

Kungiyar bayar da agaji ta duniya Red Cross, ta yi kiran da a kawo karshen wahalhalun da yakin Isra'ila da kungiyar Hamas ke haddasa wa a kan fararen hula musamman kananan yara.

Yau ne dai aka cika wata guda ta tashin rikicin wanda ya biyo harin ba zata da kungiyar Hamas ta kai Isra'ila a ranar bakwai ga watan jiya, wanda ya salwantar da rayukan mutane sama da dubu da 400.

Jim kadan bayan nan kuma Isra'ila ta kaddamar da hare-haren ramuwar gayya, da kawo i yanzu aka rasa sama da mutum dubu goma a Zirin Gaza, kamar yadda ma'aikatar lafiya da ke karkashin Hamas ta tabbatar.

A cewar kungiyar Red Cross wahalhalun da luguden wuta da ake gani a kan fararen hula a Gaza, za su haddasa matsaloli ne da za a kwashe tsawon lokaci mutane na fama da su.

Kungiyar dai na bayyana takaici kan yadda yakin ke shafar musamman kananan yara da ba su tsokani kowa ba, inda sama da yaran dubu hudu suka mutu ya zuwa yanzu.