1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Za a kawo wa Najeriya rigakafin corona a Janairu

December 17, 2020

Najeriya na fatan samun kashin farko na alluran rigakafin corona a watan Janairu mai kamawa. Ministan Lafiyar kasar Osagie Ehanire ne ya tabbatar da hakan a ranar Laraba.

https://p.dw.com/p/3mqIu
Deutschland | Coronavirus | Impfstoff
Hoto: Dado Ruvic/REUTERS

Ministan kiwon lafiyar Najeriya ya ce kawo yanzu bai san kamfanin rigakafin da Najeriya za ta kawo kasar ba. Ya ce Najeriya na cikin wata tattaunawa da kamfanonin da suka sarrafa rigakafin coronar a Birtaniya  da Rasha, to amma ya ce kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ta ba Najeriya shawarar amfani da rigakafin corona ta wani kamfanin kasar Chaina.

Ministan Lafiyar na Najeriya ya ce babu alamun za su yi amfani da rigakafin da kamfanonin Pfizer/BioNTech suka sarrafa domin kasar ba ta da zarafin samar da yanayi mai tsananin sanyi da rigakafin ke bukata a wurin ajiya.