Rikici a jam´iyar masu sassaucin ra'ayi ta FDP a Jamus
April 3, 2011Ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle ya yanke shawarar sauka daga shugabancin jam´iyarsa ta FDP mai ƙawance da jam'iyar CDU a jan ragamar gwamnati.
Westerwelle yayi wannan huruci ne a wannan Lahadin a birnin Berlin, ya na mai cewa:
Yau rana ce ta musamman gare shi, wannan shawara da ya yanke ta na bisa hanya, domin za ta baiwa matasa sabon jini, damar ɗaukar shugabancin jam´iyar FDP tare da ƙara mata ƙarfin gwiwar ci gaba da bunƙasa.
Matakin da Westerwelle ya ɗauka na da nasaba da sukar da ya ke sha daga magoya bayan FDP, game da yadda jam´iyar ke fuskantar babban koma baya, musamman a zaɓen majalisun dokokin wasu jihohi guda biyu a makon da ya gabata, inda darajarta ta faɗi warwas.
Amma Westerwelle ya ce zai ci gaba da riƙe muƙaminsa na ministan harkokin wajen Jamus.
A watan Mayu na wannan shekara FDP za ta zaɓi sabon shugaban da zai maye gurbin Guido Westerwelle.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Mohammad Nasiru Awal