1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rudanin siyasa tsakanin masu mulkin Najeriya

August 8, 2018

A ci gaba da gwawarmayar neman tasiri ga makomar shugabancin Najeriya a shekara mai zuwa an shiga kwana na biyu cikin rudanin neman sauya shugabancin majalisar kasar.

https://p.dw.com/p/32r0Z
Nigeria Bukola Saraki
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Shi kansa taron majalisar zartarawar mako-makon da kan dauki sa'o'i bakwai zuwa sama dai ya kare ne a cikin tsawon sa'o'i biyu kacal. Kuma babar hujja a fadar majiyoyin fadar gwamnatin kasar dai na zaman sauraron wani taron manema labarai na shugaban majalisar dattawa Abubakar Bukola Saraki  da nufin sanin mataki na gaba a cikin rikicin da ke neman tasiri  har a cikin fadar gwamnatin kasar inda kan 'yan majalisar zartarwa ke nuna alamu na rabewa.

Duk da cewar dai sun ki fitowa fili da nufin bayyana ra'ayinsu game da mataki na shugaban kasar da ke riko na sallamar babban jami'in hukumar tsaron farin kaya tare da kame shi.

Nigeria Präsident Muhamadu Buhari
Hoto: Novo Isioro

Ra'ayi dai na banbanta har a tsakani na ministoci na gwamnatin game da batu na sallamar Lawal Musa Daura bayan zargi hannu wajen tura jami'an farin kayan ya zuwa harabar majalisar dokoki. A saboda haka shugaban kasar da ke riko na da cikakken ikon zartawa na shugaban kasa.

Ita kanta jam'iyyar APC ta shugaban kasar dai tai juyin yar tsala wajen nuna goyon baya a bisa duk matakan da ya dace da nufin tabbatar da kai karshen shugabancin na Saraki a majalisar dattawa mai tasiri. To sai dai kuma ana samun cin karo da juna kan ra'ayi har a cikin APC inda gwamnonin jam'iyyar ke tir da matakan na jami'an tsaron da a cewar Abdul'azeez Yari Abubakar da ke zaman gwamnan Jihar Zamfara sun saba da tunanin 'yan mulki na kasar.