1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici ya jefa jam'iyyar APC cikin garari

February 17, 2023

Mako guda kafin a gudanar da babban zabe a Najeriya, rikici ya barke a tsakanin jiga-jigan jam'iyyar APC da ke zargin shugaban kasar da kokarin rushe dimokuradiyyar da ta bashi damar mulki a kasar.

https://p.dw.com/p/4Neln
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya da Bola Tinubu dan takarar shugaban kasaHoto: Nigeria Prasidential Villa

A lokaci irin wannan dai, ana dabarar kai wa ga zuwa nasarar babban zaben da ke gaban jam'iyyu a cikin Najeriya. Sai dai a jam'iyyar APC da ke da fatan dorawa bisa mulki dai, rikici ya yi nisa a tsakanin jiga-jigan jam'iyyar da ke kokarin nunin yatsa a tsakanin juna. Kama daga gwamnan jihar kano zuwa na kaduna da dan karamin kanensu da ke a jigawa dai, lokaci da suka dauki lokaci suna wa shugaba kasa biyyaya amma kuma ke zarginsa da kokarin rushe tsarin da ya ba shi damar mulki a kasar. Bayan kaucewa ta lokaci mai nisa, gwamnonin sun fito suna nunin yatsa ga Buhari da tun da farkon fari ya yi tsayuwa irin ta gwamin jaki bisa sauya kudin kasar a yayin zabe.

Nigeria Wahlen 2023
Zaben Najeriya ya zo wa jam'iyyar APC a hagunceHoto: Pius Utomi Ekpei/AFP

Wadannan kalaman na zaman ba sabun ba ga wasu a ciki jam'iyyar APC da suke da al'adar duke kafin iya hannu da shugaban kasar Muhammadu Buhari. Hon Magaji Dau Aliyu da ke zaman jigon jam'iyyar a jihar Jigawa ya ce bore da kila nunin yatsar gwamnonin na nuna halin ko- in- kula ta shugaban kasar da harkokin APC.

Daga dukkan alamu rikicin APC na rabuwar kai tsakanin kusoshi na zaman barazana mai girma a tsakanin masu tsintsiyar a halin yanzu. Duk da zagaye na shugaban kasar cikin neman kuri'a, shugaba Buhari bai boye fifita batun zabe na sahihi maimakon nasara ta masu tsintsiyar a daukacin zabuka na kasar ba.

Nigeria Änderung der Wähung Naira
Rikicin canjin kudin Naira ya jawo rikici a jam'iyyar APCHoto: Ubale Musa/DW

Nasara a cikin rikici ko tangal-tangal a cikin mayen rashin kudi dai, sabon rikicin kuma a fadar Faruk BB Faruk da ke sharhi cikin batun na siyasa na nuna alamun karshe na masu tsintsiyar da suke da burin dorawa zuwa sabuwar takwas. Ana sa ran martani daga fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa jerin zargin gwamnonin jam'iyyar da kila ma makoma ta gaba ga shugaban kasar da ke tabbatar da ritaya daga harkokin siyasa bayan kammala zabukan da ke tafe.