1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici ya ki cinyewa tsakanin Talon da Janar Tiani

Gazali Abdou Tasawa MAB
June 10, 2024

Gwamnatin Nijar ta sanar da daukar matakan da suka dace domin karbo manyan jami’anta da hukumomin Benin suka kama. Sai dai ana samun sabani kan yadda hukumomin sojin Nijar ke tunkarar rikici tsakaninta da makwabciyarta.

https://p.dw.com/p/4gsfv
Kombobild: Patrice Athanase Guillaume Talon und General Abdourahamane Tiani
Hoto: Yanick Folly/AFP/Getty Images, ORTN/TÈlÈ Sahel/AFP

Sannu a hankali, zukata na kara tafasa yayin da bakaken maganganu ke yaduwa daga shugabannin kasashen biyu makwabtan juna na Jamhuriyar Nijar da Jamhuriyar Benin har ya zuwa magoya bayansu. A sanarwar da ta fitar, gwamnatin mulkin soja ta Nijar ta sha alwashin yin amfani da duk matakan da suka dace wajen kwato jami'an kasar biyar na kamfanin WAPCO wadanda gwamnatin Benin ta  tsare da su a bisa zargin shiga kasarta ba a kan ka'ida ba. Hasali ma, a ci gaba darikici da juna, Benin ta bayyana wasun 'yan Nijar a matsayin 'yan ta'adda da ke barazana ga tsaron lafiyar kasar Benin.

Karin bayani: Benin ta zargi Nijar da toshe kafar tattaunawa

  A yayin da wasu 'yan Nijar ke jinjina wa matakin gwamnatin kasar na nuna tsauri ga kasar Benin, wasu 'yan kasar na zargin shugabannnin NIjar da nuna rashin dattaku a cikin lamarin. Sai dai wasu masu goyon bayan hukumomin mulkin sojin Nijar irin su Malam Namaiwa Ibrahim na kungiyar MPCR na daga cikin masu zargin kasar ta Benin da zama kanwa uwar gami a cikin rikicin. Amma  wasu ‘yan Nijar na ganin matsayar da hukumomin Nijar suka dauka ba ita ce mafi a'ala ba, kamar yadda Mahamadou Abdoulkader Maidalili mai adawa da mulkin soja a Nijar ya bayyana.

Mazauna Malanville a kan iyaka tsakanin Nijar da Benin na cin karo da kalubale
Mazauna Malanville a kan iyaka tsakanin Nijar da Benin na cin karo da kalubaleHoto: AFP/Getty Images

Karin bayanNijar ta jaddada ci gaba da rufe iyakarta da Benini: 

Souleiman Brha wani dan jarida ne kuma dan fafutika a Nijar ya nuna damuwa kan yadda kungiyoyi da kasashen duniya suka zura ido suna kallon Nijar da Benin na neman cin junansu. Sai dai wasu mawakan zamani na kasashen biyu na Nijar da Benin sun fitar da wata wakar hadin gwiwa ta tunatar da dangantakar tarihin da ta hada kasahen biyu tare da yin kira da a samar da sulhu tsakanin kasashen biyu.