Rikicin ficewa daga Ecowas da fadan Kwango a jaridun Jamus
February 2, 2024Jaridar die Tageszeitung ta wallafa sharihi mai taken "A halin yanzu Afirka ta Yamma ta kasu gida biyu: Mali da Burkina Faso da Nijar wadanda ke karkashin gwamnatocin mulkin soji sun fice daga cikin kungiyar raya tattalin arziki ta kasashen yankin yammacin Afirka." Kungiyar ta Ecowasmai mambobi 15, wacce aka kafa shekaru 49 da suka gabata, ta kasance ‘yar kora ta kasashen yammacin duniya tare da cin amanar ka'idojin kafa ta, wanda ke zama barazana ga mambobinta, a cewar wata sanarwar hadin gwiwa da gwamnatocin soja guda uku suka fitar.
Karin bayani: Kalubalen tattalin arziki ga ECOWAS
Kakakin gwamnatin Mali ya bayyana a gidan talbijan na kasar inda ya nuna da cewar Faransa ce ta kara rura wutar rikici a yankin na Sahel bayan dauki da ta kai wa Mali a shekara ta 2012 domin yakar 'yan tawaye wacce ta ce, ta yi amfani da wannan damar domin kara haddasa wutar rikicin. Wannan mataki ya haifar da kyamar Faransa, wanda a karshe ya janyo da juyin mulkin soja a kan zababbun gwamnatoci wadanda ke goyon bayan kasashen Yamma, samamakon yadda ayyukan ta'addanci na masu jihadi suka yadu a yankin na Sahel ciki har da Nijar da MaliNijar da Mali.Wannan ya sa an samu asarar dimbin rayuka yayin da mutane fiye da miliyan uku suka ficce daga matsugunasu.
SADC ta girka rundunar magance rikicin Kwango da kungiyar M23
''Yaki gadan-gadan a kudancin Afirka'' da haka ne jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta bude sharhin da ta wallafa kan yunkurin da kasashen yankin kudancin Afirka suka yi na tura dakarun rundunar shiga tsakani a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango. Wannan yakin da aka dade ana yi tsakanin dakarun gwamnatin da na kungiyar M23 na shirin kawo karshensa da sabuwar rundunar shiga tsakani daga kudancin Afirka ta kai a gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango. Kimanin sojoji 300 daga Tanzaniya sun sauka a lardin Goma na gabashin Kwango tare da sojoji daga Afirka ta Kudu da Malawi a karkashin umarnin kungiyar SADC da ke zama Kungiyar kasashen yankin kudancin Afirka' domin ganin ta kawo karshen fadan.
Karin bayani: Fada ya tsananta a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango
Wannan rikici na gwamnatin Kwango da kungiyar M23, wani bangare ne guda daya kacal a cikin jerin tashin hankali da aka kwashe shekaru da dama ana gwabzawa a gabashin Kwango a yankunan Ituri da Arewacin Kivu da Kivu ta Kudu tun bayan yakin farko na Kwango a shekarar 1996. Kungiyar ta M23 da aka kirkira bayan yakin Kivu ta kunshi tsaffin ‘yan tawayen CNDP da wasu sojojin Kwango, bayan yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla da Kinshasa a ranar 23 ga watan Maris na shekara ta 2009, kungiyar ta sake daukar makamai a shekara ta 2012.
Kasashen Turai na kokarin dakile kwararar bakin haure daga Afirka
Sai Jaridar Tagesspiegel wacce ta wallafa labarin kokarin da nahiyar Turai ke yi na kulla yarjejeniyar kaura da Afirka domin yaki da bakin haure.Firaministar Italiya Giorgia Meloni ta gabatar da wata yarjejeniya ga abokan huldarta na Afirka, a taron kasashen Afirka da aka yi a birnin Roma na Italiya, wanda ya samu halarta shugabannin guda 45 wadanda za a bai wa kasahensu karin tallafi na kusan Euro biliyan 5.5 wanda za a yi amfani da shi wajen inganta ayyukan samar da makamashi.
Karin bayani:Nijar: Bai wa bakin haure damar wucewa Turai
Za a samar da tallafi ne ga kasashen Afirka wajen aiwatar da alkawurran zabe da suka yi da daukar matakan kariyar kaura ba bisa ka'ida ba ta ruwan teku, alkawarin da har yanzu ake ganin cewar akwai sabawa a ciki. A bara kawai, ‘yan gudun hijira 157,600 suka kwarara zuwa Italiya idan aka kwatanta da dubu 103,000 a shekarar ta 2022.