1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaMozambik

Yuwuwar samun tashin hankali kan sakamakon zaben Mozambik

Antonio Cascais Abdulkarim Muhammad Abdulkarim/SB
October 23, 2024

A kasar Mozambique ana ci gaba da dakon jiran sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar ranar 9 ga watan Oktoba da mu ke ciki, wanda ya kamata a sanar da cikekken sakamakon daga yanzu zuwa ranar Jumma'a.

https://p.dw.com/p/4m9Zt
Mozambik | Zanga-zanga
Zanga-zanga a MozambikHoto: Alfredo Zungia/AFP

A kasar Mozambique ana ci gaba da dakon jiran sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar ranar 9 ga watan Oktoba da muke ciki, wanda ya kamata a sanar da cikekken sakamakon daga yanzu zuwa ranar Juma'a, 25 ga watan, kamar yadda dokar zaben kasar ta yi tanadi. Yayin da masu saka ido kan yadda zaben ya gudana suka hakikance cewa 'dan takarar jam'iyyar FRELIMO mai mulkin kasar Daniel Chapo za a sanar a matsayin wanda ya samu nasara, duk da tarin korafe-korafen da 'yan adawa ke yi na magudin zabe.

Karin Bayani: 'Yan adawa sun yi zargin tafka magudi a zaben kasar Mozambik

Mosambik, birnin Maputo I Zanga-zanga
Zanga-zanga a MozambikHoto: Siphiwe Sibeko/REUTERS

Gabanin fitar da sakamakon zaben ne wasu 'yan bindiga suka halaka babban lauyan jam'iyyar adawa ta Podemos Elvino Dias, da kuma wani babban jigonta Paulo Guambe, bayan bude musu wuta suna tsaka da tafiya a mota a Maputo babban birnin kasar, wadanda suka taka gagarumar rawa wajen ganin 'dan takararsu Venancio Mondlane ya samu nasarar lashe zaben kasar, don maye gurbin shugaba mai ci na jam'iyyar FRELIMO Filipe Nyusi, wanda ke kammala wa'adin mukinsa na zango biyu, bayan haye wa kan karagar mulki tun a shekarar 2015. Kuma jam'iyyarsa ta FRELIMO na rike da madafun ikon Mozambique tun a shekarar 1975, bayan samun 'yancin kai daga Portugal.

Mozambik | Zanga-zanga
Zanga-zanga a MozambikHoto: Alfredo Zungia/AFP

Kasar ta fada cikin rudani da zaman dardar bayan kisan wadannan jiga-jigai na jam'iyyar adawa, inda 'dan takararta na shugaban kasa Venancio Mondlane ya zargi jami'an tsaron kasar da aikata wannan kisan gilla, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na facebook. Wannan matsala ta janyo martani mai zafi daga fannoni da dama da masu bibiyar siyasa da harkokin kare hakkin 'dan adam.

Kisan mutane a lokacin hada-hadar siyasa a kasar Mozambik dai ba sabon abu ba ne, domin ko a cikin shekarar 2015 da kuma 2019 an halaka 'yan jarida da 'yan gwagwarmaya da sauran kwararru a cikin al'umma, wanda ake zargin 'yan siyasa da kulla wannan manakisa. Kisan da ake yi wa 'yan adawa a kasar ya samu suka sosai daga kungiyar tarayyar Turai EU da Amurka da kuma kungiyar hadin kan kasashen Afirka AU, har ma da Majalisar Dinkin Duniya, wadanda suka bukaci da a hanzarta gudanar da bincike domin zakulo masu aikata laifukan, tare da hukunta su.