1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

'Yan bindiga a Mozambik sun halaka 'yan adawar gwamnati

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
October 19, 2024

Ana sa ran sanar da cikakken sakamakon ne a ranar 24 ga watan na Oktoba, kuma yau sama da shekaru 25 kenan da Frelimo ke jagorantar kasar

https://p.dw.com/p/4lzBp
Hoto: PODEMOS

Wasu 'yan bindiga a Mozambik sun halaka manyan jiga-jigan 'yan adawar gwamnati biyu, bayan bude musu wuta suna tsaka da tafiya a mota a wannan Asabar, lamarin da ya kara jefa kasar cikin fargabar barkewar rikici, gabanin fitar da kammalallen sakamakon zaben shugaban kasar.

Karin bayani:Al'ummar Mozambique na kada kuri'a a zaben shugaban kasa

Wata kungiya mai rajin kare hakkin 'dan adam kuma mai bibiyar al'amuran siyasar kasar, ta ce harin ya faru ne a yankin Bairro Da Coop da ke kusa da Maputo babban birnin kasar, inda maharan suka harbe lauyan jam'iyyar Podemos Elvino Dias, da kuma kusa a cikinta Paulo Guambe.

Karin bayani:Mutane 8 'yan gida daya sun mutu bayan kifewar kwale-kwale a Mozambique

Podemo da 'dan takararta na shugaban kasa Venancio Mondlane, sun ki amincewa da sakamakon zaben da ke nuna cewa 'dan takarar jam'iyyar Frelimo Daniel Chapo ne ke shirin lashe zaben, wanda aka gudanar ranar 9 ga wannan wata na Oktoba. Ana sa ran sanar da cikakken sakamakon ne a ranar 24 ga watan na Oktoba, kuma yau sama da shekaru 25 kenan da Frelimo ke jagorantar kasar.