Rikicin kasuwanci tsakanin Amurka da Yuganda
November 6, 2023Shugaba Yoweri Museveni na kasar Yuganda, ya ce Amurka ta kai kanta matsayin da ba ta kai ba a idon kasar Yuganda idan tana tunanin za ta iya kassara ci gabanta.
A makon jiya ne dai Amurkar ta tsame kasar ta Yuganda daga cikin yarjejeniyar kawancen cinikayya a tsakaninta da kasashen Afirka, matakin da zai fara aiki daga badi.
Manufar yarjejeniyar ita ce dauke wa kasashen Afirka da ke cikin tsarin AGOA harajin shigar da kaya Amurka, musamman kasashen da ke bin tsarin dimukuradiyya sau da kafa.
Kasar Yuganda dai na shan suka daga kungiyoyin kare hakkin bil Adama da Majalisar Dinkin Duniya da ma kasashen yammacin duniya, saboda dokar hukunta masu neman jinsi da ta kafa a cikin watan Mayu.
Sai dai duk da matakin na Amurka, Shugaba Yoweri Museveni, ya shaida wa 'yan Yuuganda cewa su kwantar da hankalinsu game da abin da gwamnatin Amurkar ta yi.
Shi ma bankin duniya, ya sanar da matakinsa na dakatar da bai wa Yuganda rance cikin watan Agustan da ya gabata.