Rikicin kasar Zimbabuwe da zaben Najeriya a jaridun Jamus
January 25, 2019Jaridar Die Tageszeitung wadda ta yi tsokacin kan zanga-zanga a kasar Zimbabuwe tana mai cewa bayan arangama tsakanin jami'an tsaro da masu zanga-zangar nuna adawa da farashin man fetur yanzu Shugaba Emmerson Mnangagwa da kanshi ya ce zai magance matsala yayin da a can birni Bulawayo kuma jami'an tsaro ke farautar wadanda ake zargi da angiza mutane su yi bore. Jaridar ta ce Shugaba Mnangagwa ya katse rangadin da yake a kasashen ketare ya koma gida babu shiri inda da saukarsa a ranar Litinin ya ce zaman lafiya suke so da hadin kan ‘yan kasa yana mai cewa duk mai korafi ya na da ‘yancin mika kuka a hanyar da doka ta tanada, amma ba daukar doka a hannu ana lalata kadarorin kasa da na al’umma ba.
Ita ma jaridar Neue Zürcher Zeitung ta yi sharhi kan kasar ta Zimbabuwe tana mai cewa farashin man fetur mafi tsada a duniya ya janyo bore. Ta ce karin farashin man fetur a Zimbabuwe daga dala 1.24 zuwa fiye da dala uku kowacce lita da ya fara aiki daga ranar 13 ga watan nan na Janeru, ya janyo hauhawar farashin kaya lamarin da ya gamu da fushin al'umma. Jaridar ta kara da cewa shekara guda da ta gabata an yi kyakyawan fata bayan da gwamnati ta ba wa masu zuba jari na ketare izinin shiga kasar da ta ce ta bude kofofinta ga kamfanoni na ketare, amma zaben da ya biyo baya da ake takaddama kai da kuma tashe-tashen hankulan da kasar ke fuskanta yanzu ya kawar da fatan samun kwanciyar hankali da lumana a Zimbabuwe.
Yakin neman zabe na nuna fuskoki maimakon manufofi na hakika a cewar jaridar Die Tageszeitung a labarin da ta buga dangane da zaben da ake shirin gudanarwa a Najeriya ranar 16 ga watan Fabrairu. Ta ce dukkan ‘yan Najeriya na magana game da tattalin arziki, tsaro da cin hanci da rashawa amma ana rashin wata sahihiyar muhawara a kan wadannan batutuwa. ‘Yan takara sun dukufa wajen yi wa juna yarfe a duk lokacin da suka tsaya kan dandamalin yakin neman zabe, maimakon su mayar da hankali yadda za a magance matsalolin da suka fi ci wa al'ummar Najeriya tuwo a kwarya wato rashin tsaro da cin hanci da rashawa da inganta ginshikan tattalin arziki da ilimi da kuma kirkiri guraben aikin yi ga matasa.
A karshe sai jaridar Süddeutsche Zeitung wadda ta ce mataimakin firaminstan Italiya Luigi Di Maio ya soki lamirin kasar Faransa da zama musabbabin matsalolin da kasashen Afirka da ta yi wa mulkin mallaka ke ciki. Mista Di Maio ya ce yadda Faransa ke buga wa kasashen Afirka 14 da ta yi wa mulkin mallaka takardun kudinsu na CFA ya hana su ci-gaba, ya ce wannan nema ya taka rawa a kwararar ‘yan gudun hijira. Faransa dai ta yi watsi da zargin. Jaridar ta ce kalaman na matamakin firaministan kasar ta Italiya sun samu karbuwa a Afirka musamman dangane da kudin na CFA da farin jinsa ke kara dusashewa a Afirka.