Bayyanar kungiyoyin siyasa a Najeriya
February 22, 2022Kama daga tsofaffin gwamnoni ya zuwa ga ministoci da kila ma 'yan bokon da ke fadin tayi baki dai, ra'ayi yazo iri guda bisa bukatar sauyi cikin fagen siyasa ta kasar.
Kuma a tsakiya ta karatun dai na zaman kokari na kwace goruba a hannun kuturu bayan abun da suka kira gazawar manyan jam'iyyun kasar guda biyu.
A karakashin kungiyar National Movement da kuma jagorancin tsohon gwamnan jihar Kano Rabi'u Musa Kwankwaso, wasu jiga jigai na siyasa ta kasar dai sun ce akwai bukatar ceto ga kasar dake a halin rudu yanzu. Farfesa Rufa'i Alkali dai na zaman tsohon kakakin jam'iyyar PDP ta adawa.
" In kasar nan ta kama wuta kowa sai yaji a jikinsa. Yanzun ma akwai wuraren da za'a ce ai yaki ya cinyesu a jihohi daban daban. Da muna maganar yankin Arewa maso Gabashi yanzu mun koma Arewa maso Yammaci, Kudu maso Kudu suna kukaKudu maso Gabashi suna kuka. Shi yasa lokacin da muka fara tafiyar nan bamu bar kowa ba, mu ce ka cigaba da zama a jam'iyyarka amma kuma kazo mu tafi. In lokaci yayi na yanke hukunci, sai mu yi shawara wace tafiya za'a yi. Amma dai yanzu jiki ne a hankalinsa na wata”.
Gangar jiki cikin PDP ruhi a cikin sabon tsarin dai, taron da ke zaman irinsa na farko ya gaza kaiwa ga samun jiga jigai irin nasu tsohon shugaban hukumar zabe Farfesa Attahiru Jega da kuma abokan takun da tun da farkon fari aka rika ta'allakawa a cikin sabon tsarin.
To sai dai kuma duk da cewar dai sun ce suna nan a cikin jam'iyyun gado, daukacin mahallarta taron dai sun ce suna shirin su yada kwallo na mangwaro da nufin kaucewa kudan da ke ta mamayar manyan jam'iyyu na kasar yanzu. Solomon Dalung dai na zaman jigo a cikin jam'iyyar APC:
"Ni ba jam'iyya nake bi ba. Ni ina bin abun da zai kawo ci gaba da gina kasar nan. Saboda haka in jam'iyyata ta APC bata iya haifar da mai ido ba, ba zamu cigaba da haihuwar makafi ba. APC da PDP dan juma ne da dan jummai, siyasa daya ne sunayensu ne daban daban. Ai wadanda suke APC jiga jigan ai lokacin da muka shigo muna tuhumarsu da cin hanci, har EFCC ta gurfanar dasu gaban kotu, amma yanzu sun zama ministoci, an zabi gwamna fa yana bacci, kotu ce ta tashe shi ta ce kazo ka zama gwamna. Da ya gama rantsuwa ya zubar da mutane ya tuba ya zama dan APC”.
To sai dai kuma a cikin neman sauyin dai, masu takama da siyasar basu boye abun da ke a zuciyar da dama a cikin 'yan taron ba.
Kuma daya bayan daya dai sun rika fitar da maitar da ke a zuciya tare da neman fitar da Kwankwason Kanon domin jagorantar tafiyar a zabe na shugaban kasar dake tafe. Matsayin kuma da daga dukkan alamu ya dadada rai na tsohon gwamnan na Kano.
" In mutun ya tashi ya ce ga ra'ayinsa to shikenan in abun dadi ne sai kaji dadi sai ka duba in abun alheri kake yi to sai ka kara, in kuma maras kyau kayi to sai ka dubi abun da yasa ya fadi haka kuma sai ka gyara.”
Abun jira a gani dai na zaman yadda take shirin da ta kaya a tsakanin masu tunanin sauyin da masu kallon dama a cikin neman sauyin.