Rundunar sojin Jamus ta Bundeswehr ta sami kanta cikin wata taɓargaza.
October 27, 2006Ga babban jami’in gwamnatin tarayya mai kula da harkokin rundunar sojin Jamus ta Bundeswehr, Reinhold Robbe dai, babu shakka dakarun Jamus sun wuce gona da iri a Afghanistan, game da wannan batun da ake ta ƙorafi aknsa yanzu, inda aka buga hotunan wasu sojojin rundunar ɗauke da ƙoƙon kan mutum. Kamar dai yadda ya bayyanar:-
„Kawo yanzu dai, ta yin la’akari da matsayin da aka kai a binciken da ake gudanarwa kan wannan batun, za a iya cewa, sabbin hotunan da aka samun ma, sahihai ne, wato ababa ne da suka wakana a zahiri.“
Duk da tifin Allah tsinen da babban sifeton rundunar sojin ta Bundeswehr, Wolfgang Schneiderhan, ya yi wa wannan mummunan aikin, ya ce ba za a iya shafa wa sunan rundunar gaba ɗaya kashin kaza ba. Akwai dai ’yan ɓata gari a cikin sojojin rundunar, amma bai kamata a yi ta zargin rundunar gaba ɗaya ba, inji shi.:-
„Har ila yau dai, ina nanata jawabin da na yi tun da farko na cewa, wannan batun bai shafi duk dakarunmu ba. Wasu ’yan tsiraru daga cikinsu ne kawai suka goce daga tsarin nuna kyawawan halayyar da muka horad da su. A nawa lissafin dai, a cikin wannan sabon hoton ma, sojoji uku kawai muke gani. Idan muka haɗa su da na waɗanda Bildzeitung ta buga, wato mun sami dakaru 9 ke nan. To idan kuwa aka yi la’akari da yawan dakarunmu dubu 8 da ɗari 5, da ke girke a ƙetare, za a ga cewa, waɗanna guda taran, wato tsiraru ne.“
Jaridar ta Bildzeitung dai ta yi fira da ɗaya daga cikin sojojin da ke kan hotunan da ta bugan. Bisa bayanasa da ya bayar, ba a maƙabarta aka ɗau hotunan ba. A wani gun ɗebo yashi na gini ne aka ɗauke su. Babu dai wanda ya tilasa musu ɗaukar hotunan da ƙoƙon kann mutum. Sai dai wasu ’yan rukunin da ba su bari an ɗauke su ba, daga baya an yi ta musu barkwanci ne kamar raggwaye.
Babban sifeton rundunar, Robbe, ya ƙara bayyana cewa, kamata ya yi dai a sake nazarin irin horon da ake bai wa sojojin kafin a tura su zuwa aikin wanzad da zaman lafiya a ƙasashen ƙetare:-
„Tambaya a nan ita ce, ko an bai wa dakarun cikakken horo, musamman a huskar siyasa, wadda ita ce ke da muhimmanci a wannan lamarin ? An bayyana musu irin darajar da muke bai wa aƙidojinmu, waɗanda ke da muhimmanci a nan kamar a inda aka girke su ? A wane matsayi muke, wajen ba su horo na tushe, game da kiyaye hakkin ɗan Adam ?“
Duk waɗannan tambayoyin dai kamata ya yi a bi diddiginsu. Babban sifeton dai ya ce zai gudanad da cikakken bincike kan wannan batun, kuma za a hukuntad da duk waɗanda aka samu da aikata laifuffuka:-
„Kamata ya yi dai sojoji su san iyakar ’yancin da suke da shi, su kuma san hakkinsu da abin da za su iya aikatawa ko kuma aka haramta musu. Bayan haka, idan suka keta doka ko suka take hakkin wani, to wannan ba abin da za a yi musu afuwa ba ne.“
A majalisar dokoki kuma, wani ɗan majalisar na jam’iyyar Greens, Hans-Christian Ströbele, ya ce ya sami labarin akwai hotuna da dama na ɓatanci da sojojin Jamus ke ɗauka, yayin aikinsu a ƙetare. To hakan dai zai iya janyo taɓargaza, idan irin waɗannan hotunan suka shiga hannun ’yan jaridu har kuma aka buga su.
„Ina dai fargabar cewa, har ila yau za a sake buga wasu hotunan kuma a bainar jama’a, saboda na sami labarin cewa, ’yan rukunin KSK da aka girke a Afghanistan, sun ɗau irin waɗannan hotunan da dama, waɗanda kuma ke ƙunshe da ababan da za su iya haifad da matsaloli da yawa idan anm buga su.“
A halin yanzu dai, ba a san lokacin da za a zo ga ƙarshen wannan muhawarar ba. Saboda babu shakka, sauran kafofin yaɗa labarai, za su dinga buga ire-iren waɗannan hotunan idan sun same su, abin da kuma zai ƙara yayata taɓargazar.