Rusau ya jefa talakawa cikin kunci a Lagos
April 12, 2017A kokarin jihar Lagos na zama birni da a turance ake kira "Mega city" ta dauki mataki na kakkabe matsugunan da aka gina ba bisa ka'ida ba, musamman wadanda suke kusa da bakin teku ko kuma wurare da ke da kusanci da abun da ake kira Lagoon a turance. Ko da a wannan watan da ya gabata sai da talakawan gari suka rasa gidajensu duk kuwa da dakatar da rusau da kotu ta yi bisa kokarin mazauna yankunan .
Madame Megan Chapman ta kasance shugabar wata kungiya ta rundunar adalci a Najeriya wacce a turance ake rira da suna Justice and Empowerment Initiative ta ce a bincike da suka gudanar sun gano cewar "tun daaga lokacin da aka yi wannan rusau a karshen shekrarar bara zuwa yau masu gidajen suna ta watangaririya, sun rasa makoma, wanda hakan bai dace ba."
Sai dai a cewarta babu tarnakin da ya wuce karan tsaye ga kin bin umarnin kotu na dakatar da rusau. Ta ce "da zarar da kotu ta bayar da umarnin dakatar da wannan rusau a a ranar 7 ga watan Nuwamban bara, gwamnati ta ci gaba da rusau musamman a otode Bgami."
Ko mene ne matsayin kungiyar da ke fafutukar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International? Kakakin Kungiyar a Najeriya Alhaji Isa Sunusi ya ce "Kungiyar Amnesty bata da buri in ka dauke tabbatar da adalci a tsakanin al'umma ba tare da danne hakkin marasa karfi ba."
Seye adejo dalibi ne a makarantar sakandare kuma mazauni a irin wadannan wurare. ya ce "ko kadan hakan babu kyau sabili da dama wasu yaran anan aka haifesu kuma basu da wurin zuwa."
Shi kuwa Abdulrahaman Adamu cewa ya yi batun babu lissafi a ciki , saboda "idan dai har ana son adalci to kamata a samar masu da inda zasu zauna, amma in haka ko kadan bai dace ba ga kasa irin tamu a Najeriya."
A kowane lokaci gwamnati na cewa tana daukar mataki ne don tabbatar da tsaro da kuma kawata birnin lagos a matsayinsa na cibiyar kasuwancin Najeriya.