Sokoto: Yaki da 'yan bindiga masu yin garkuwa da mutane
September 4, 2024Zuwan karamin ministan tsaro na Najeriya Bello Muhammad Matawalle da shugaban hafsan hafsoshin tsaro na kasa Janar Christofa Musa a Jihar Sokoto, na nuna irin yadda gwamanatin Najeriya ke kokarin kakkabe ta'addanci da fatan ta kawo karshen matsalar rashin tsaro da aka kawashe sama da shekaru goma ana fama da ita a arewacin Najeriya. Ministan tsaron ya yi karin haske ga gwaman jihar a kan makasudin isowar su Jihar ta Sokoto.
‘'Mai girma shugaban kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya umurce mu da cewa mu zo Sokoto domin mu tabbatar da cewa ta kowane hali da ake ciki an tabbatar da an samu tsaro cikakke a wannan yanki, da kuma abun da ya biyo baya wanda muka samu matsala a Sabon Birni''. Shi ma dai gwamnan Jihar Sokoto Ahmed Aliyu ya yi bayani a kan mara baya da gwamnati za ta yi ga wannan tafiya, ta dakarun Najeriya a kan aniyarsu ta kakkabe ‘yan bindiga musamman a yankin gabashin Sokoto. ‘'Ina son in shaida maka cewa gwamnatin Jihar Sokoto ta shirya tsaf ta baku duk wani irin hadin kai da goyon bayan da kuke so domin ku cimma wannan buri, ina son ka isar da sakonmu na godiyya ga shugaban kasa kuma kwamandan askarawan Najeriya kan wannan umurni da ya bayar na ku zo, ku taru, a garin Sokoto domin a tabbatar da cewa an samu tsaro da jihar.''
Kisan sarkin Gobir a gabashin Sakoto da karuwar hare-haren ‘yan ta'adda a arewacin Najeriya na daga cikin dalilai na isowar dakarun na Najeriyar a Sakoto. To amma shin ko mi al'ummar jihar za su ce: ‘'Idan za ka iya tunawa a shekarun baya an taba irin wannan , tsohun shugaban kasa Muhammadu Buhari ya je Zamfara har cikin daji ya shiga har kayan soji mun ga ya sanya, amma daga baya ba wani abu da ya biyo baya.'' Tuni masu fashin baki da sharhi a kan al'amuran tsaro a Najeriyar ke bayyana yadda suke kallon tarewar sojojin da ministan a matsayin wani abin da idan ba a dage ba, ba zai haifar da komai ba.