1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boko Haram da batun 'yan matan Chibok

Al-Amin Suleiman Mohammed/ LMJAugust 14, 2016

Rundunar sojojin Najeriya ta musanta ikirarin da kungiyar Boko Haram ta yi a sabon faifayen bidiyonta, inda ta yi zargi harin sojojin da sanadiyyar mutuwar wasu daga cikin ‘yan matan Chibok da ke hannunta.

https://p.dw.com/p/1JiCp
Sabon bidiyo kan halin da 'yan matan Chibok ke ciki
Sabon bidiyo kan halin da 'yan matan Chibok ke cikiHoto: picture alliance/AP Photo

A wata sanarwa da Birgediya Janar Rabe Abubakar kakakin rundunar tsaron Najeriya ya fitar jim kadan bayan bayyanar faifayen bidiyon ya ce ikirarin kungiyar farfaganda ne kawai domin shafawa rundunar kashin kaji. Janar Rabe Abubakar ya ce duk hare-haren da suke kaiwa suna amfani ne da makamai da ke da fasahar zuwa inda aka nufa kuma suna yakin ne bisa kwarewa.

Iyayen 'yan matan Chibok na cikin damauwa
Iyayen 'yan matan Chibok na cikin damauwaHoto: DW/A. Kriesch

Da wannan Lahadi ne dai kungiyar Jama'atu Ahlul Sunna da aka fi sani da Boko Haram ta fitar da wani sabon faifayen bidiyo da ke nuna wasu daga cikin ‘yan matan sakandaren Chibon da ta ke garkuwa da su, inda ta bayyana cewa wasu daga cikinsu sun mutu sanadiyyar hare-hare da Sojoji suka kai a inda suke zaune. A wannan faifayin bidiyo dai an nuna wani daga kwamandojin kungiyar tsaye a gaban ‘yan matan masu yawa fuskar sa a rufe kuma yana rataye da bindiga, inda ya ce ba su da wata bukata da ‘yan matan illa a sakar musu ‘yan uwansu kafin su sake su. Ya kuma bayyana halin da wasu daga cikin wadannan ‘yan matan ke ciki a halin yanzu.

Kira daga 'yn matan Chibok


An nuna daya daga cikin ‘yan matan wacce ta yi magana da harshen Hausa da kuma na Chibok din, inda ta yi kira ga iyayensu da su yi hakuri kuma su nemi gwamnati ta saki ‘yan kungiyar ta Boko Haram da ke hannunta domin suma su koma gida. Yayin da wannan yarinya ta ke magana an ga wasu daga cikin 'yan matan da ke sanye da hijabi suna share hawaye a fuskokinsu in da kuma za a iya ganin wata daga cikinsu rike da yaro wata kila wanda ta haifa.

Gangami kan a dawo da 'yan matan Chibok da Boko Haram ta sace
Gangami kan a dawo da 'yan matan Chibok da Boko Haram ta saceHoto: picture-alliance/dpa/D. Kurokawa

Nazari kan bidiyon


Iyaye da ‘yan uwan 'yan matan sun ce suna nazarin faifayen bidiyon da kungiyar ta fitar domin tabbatar da cewa ‘ya'yansu ne. A karshen wannan bidiyo dai an nuna jirgi yana shawagi a sama inda daga bisani aka nuna gawarwakin wasu mata da aka ce sune jirgin sojojin ya jefawa bam a wani wuri da suke.