Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da jirgin kasa
July 26, 2016Bayan share shekara da shekaru cikin tsohon tsari gwamnatin Najeriya ta kaddamar da sabon jirgin kasa na zamani mai gudun famfalaki.
Jirgin da zai rika jigila daga tashar Idu dake nan a Abuja ya zuwa Rigasa dake a kaduna duk dai cikin arewacin tarrayar Nageria dai na zaman irinsa na farko a cikin tarihi na kasar.
A shekara ta 2009 gwamnatin kasar ta kaddamar da shirin sauyin tsarin jirgin zuwa na zamani tare da kaddamar da kashin farko na Abuja zuwa Kaduna a karkashin wani shiri na shekaru 25 da kuma a karkashinsa kasar take neman hade garuruwa na Abuja da Kano da kuma Ibadan zuwa Legas sannan kuma da Legas ya zuwa Calaba da tsarin jirgin na zamani.
Sabon jirgin na kaduna zuwa Abuja zai fara ne da daukar kimanin mutane dubu biyu a kusan kullum a cikin sawu hudu na mutane 500 a cewar ministan sufurin kasar Rotimi Ameachi da kuma ya ce zai hada da kayan noma daga birnin na Kaduna domin amfanin mutanen birnin na Abuja.
A karon farko karamar kujera a tsakanin hanyar ta Abuja zuwa Kaduna za ta tafi a kan Naira 300 a yayin kuma da babba za ta tafi a kan Naira 600. Abin da ko bayan sauki ke kuma zai taimaka wajen rage matsalar rashin tsaron da ke zaman ruwan dare a tsakanin mabiya hanya.
Ayyuka sama da dubu 10 ne dai har ila yau sabon layin dogon ya samar a fadar Leon Li da ke zaman shugaban kamfanin kasar China na CCECC da ya gudanar da aikin ginin layin dogon.
Dalar Amirka milyan 874 da suka hada da wani bashin bankin zuba jari na kasar China na dala milyan 500 gwamnatin ta kashe wajen sabon aikin da ake yi wa kallon sabon babi a cikin harkar sufurin kasa na kasar da a baya ake yi wa kallon hanyar sata a tsakanin 'yan boko na kasar.
Harkar kuma da a cewar Shugaba Muhammadu Buhari za ta sauya ya zuwa dama ta inganta rayuwar al'ummar tudu da gangaren kasar.