1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Super Eagles ta yi sabon jagora

Aliyu Muhammad Waziri L
August 28, 2024

Masana da sauran masu bibiyar harkar kwallon kafa a Najeriya, na ci gaba da bayyana ra'ayinsu game da nadin sabon mai horas da kungiyar kwallon kafar kasar ta Super Eagles.

https://p.dw.com/p/4k1WV
Najeriya | Kwallon Kafa | NFF | Super Eagles | Bruno Labbadia
Sabon mai horas da 'yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Bruno Labbadia.Hoto: Thomas Kienzle/AFP/Getty Images

Hukumar Kula da Kwallon Kafa ta Najeriyar NFF, ta fitar da wata sanarwa ta hannun sakataren hukumar Dakta Muhammad Sanusi da ya ce nadin ya fara aiki ne nan take. Nadin na Bruno Labbadia na zuwa ne bayan da kwamitin da aka kafa da kuma dora masa alhakin zakulo mai horaswar da ya dace ya mika rahotonsa, kuma ya bayar da sunan Bruno Labbadia. Nan take dai NFF din ta amince da shi a matsayin sabon mai horas da 'yan wasa na babbar kwallon kafar kasar ta Super Eagles, wanda ya zama shi ne mai horas da kasar na 37 a tarihi. Nadin Labbadia ya zo ne a wata gaba da kasar take tangal-tangal, bayan wa'adin Finidi George na takaitaccen lokaci da ya jefa kasar cikin mawuyacin yanayi.

Najeriya | Kwallon Kafa | NFF | Super Eagles | Finidi George
TSohon mai horas da 'yan wasan kwallon kafa na Najeriya Finidi GeorgeHoto: Nigerian National Football Federation

Labbadia ya kasance Bajamushe na shida a tarihin Najeriya da ya zama mai horas da 'yan wasan na Super Eagles, duk da cewa a wannan gaba wasu na zargin nadin nasa da hukumar NFF ta yi a matsayin neman sauki ne bisa la'akari da rashin tabuka abin kirki da kungiyarsa ta Stuttgart ta yi, wato abin da wasu suke kira da neman ceto. Sai dai duk da haka wasu na da fahimtar cewa sai an ba shi lokaci kafin a iya yanke hukunci. Babban kalubalen da ke gaban sabon mai horas da 'yan wasan na Super Eagles Labbadia shi ne, neman gurbin Gasar Cin Kofin Kwallon Kafa na Kasashen Afirka AFCON a shekara mai zuwa ta 2025. Zai fara ne da kece raini da Jamhuriyar Benin a birnin Uyo a gida Najeriya ranar bakwai ga watan Satumba mai kamawa, kana ya bi kasar Ruwanda gida bayan kwanaki uku da yin wasa da Benin. Duk da kwarewar sabon mai horas da Super Eagles Labbadia mai shekaru 58 a duniya, wasu na ganin ya karbi aikin a kurarren lokaci da ba lallai a samu abin da ake tunani ba.