1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon shugaban Hukumar Zaɓen Najeriya Attahiru Jega

July 8, 2010

Farfesa Jega ya kasance tsohon shugaban ƙungiyar malaman Jami'oi ta ƙasa wato ASSU

https://p.dw.com/p/OE9k
Shugaban Najeriya Jonathan Goodluck.Hoto: AP

Shi dai Farfesa Attahiru Jega, an haife shi ne a ranar 11 ga watan Janairun 1957 a garin Jega dake jihar Kebbi ta yanzu. Kuma ya halarci makarantar firamare ta Sabon Gari a Jega, tsakanin shekarar 1963 zuwa 1969.

Bayan kammala makarantar Firamaren sa ne kuma ya shiga kwalejin gwamnati dake birnin Kebbi. Ya kuma samu shiga Jam'iar Ahmadu Bello reshen Kano daga shekarar 1974 zuwa 1979, inda ya karanci kimiyyar  siyasa.

Bayan kammalla karatun sa a Jami'ar ta Bayero yaci gaba da aikin koyarwa a jami'ar, kafin ya tafi jami'ar Northwestern dake Amirka domin samun digiri na biyu da kuma na ukku tsakanin shekarun 1981 zuwa 1984.

Farfesa Jega ya gudanar da aiyukan bincike da dama a jami'o´i da cibiyoyi daban-daban, da suka haɗa da cibiyar nazarin harkokin ƙasashen waje ta Najeriya da ke lagos da Jami'ar Stockholm a ƙasar Swiden. Ya kuma zama daraktan cibiyar Nazarin harkokin demokiraɗiya ta Jami'ar Bayero ta Mambayya, kafin zama mataimakin shugaban Jami'ar a shekara ta 2005.

A shekarar 1990 Farfesa Jega ya kasance shugaban ƙungiyar malaman jami'oi ta ƙasa wato ASSU, kuma a zamamin sa ne ƙungiyar ta ƙalubalanci gwamnatin mulkin sojan Janar Ibrahim Babangida akan inganta harkokin ilimin Jimi'o'i da kuma kyautata jindaɗin malaman makarantu.

Kafin shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya naɗa shi shugaban hukumar zaɓe ta INEC, Jega ya kasance wakili a kwamitin da gwamnatin tsohon shugaba  marigayi Alhaji Umaru Musa Yar'adua ya kafa domin bada shawara akan hanyoyin tabbatar da zaɓe na gaskiya a Najeriya wanda ke ƙarƙashin shugabancin mai shari'a Muhammad Lawal Uwais.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Yahouza Sadissou Madobi