1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaddama kan canjin dala a Najeriya

Uwais Abubakar Idris
June 1, 2023

A Najeriya babban bankin kasar ya bullo da sabon tsarin barin kasuwa ta yi halinta wajen hada-hadar sayen takardar kudi ta dala ga masu bukata.

https://p.dw.com/p/4S4CJ
Währung | Euro, Yuan und Dollar
Takardun kudaden Euro da Dala da YuanHoto: Antonio Pisacreta/ROPI/picture-alliance

Tsarin da ke cikin kokari na amfani da farashi na bai daya a saye da sayar da takardar kudin a kasar domin kaucewa masu cuwa-cuwa da cin kazamar riba ta wannan hanya.

Wannan sabon tsari ko salo na hada-hadar takardar kudin ta dallar Amurka da babban bankin na Najeriya ya bullo da ita a yanzu, ta bada dama a bari kasuwa ta yi halinta wajen hada-hadar takardar kudin maimakon kayyade farashi da a baya babban bankin ke amfani da shi.

US-Dollars und Ägyptisches Pfund
Dalar AmurkaHoto: Khaled Elfiqi/epa/dpa/picture alliance

Wannan na faruwa ne bayan da shugaban Najeriyar Bola Ahmed Tinubu ya sanar da manufarasa ta amfani da kafa da ma farashi na bai daya ga hada-hadar kudadden kasashen waje musamman dallar Amurka, wacce ita tafi daukan hankali kuma aka fi hada-hada a kanta. To sai dai matakin ya sanya babban bakin Najeriya yin karin haske a kan wannan don kaucewa tunanen da aek na rage darajar Naira.

Najeriya dai ta dade tana sauye-sauye na tsarin hada-hadar kudadden kasashen waje musamman ma dai dallar Amurka wacce masu masana'antu da sauran ‘yan kasuwa ke amfani da ita domin shigo da kaya daga kasashen waje.

Nigeria Änderung der Wähung Naira
Takardar NairaHoto: Ubale Musa/DW

Samar da farashi na bai daya wajen hada-hadar takardar kudi ta dalla don barin kauswa ta yi halinta zai taimaka bunkasa tattalin arziki inda kowa ya nufi kasuwa ba tare da fakewa da samun dalla ta hannun gwamnati a farashi mai sauki ba.