Nijar: Yaushe gwamnati za ta daina zargi?
January 16, 2025Tuni dai wannan batu y sake haifar da muhawara a kasar, Malam Bana Ibrahim na kungiyar Front Patrotique na daga cikin wadanda suka yi imani da zarge-zargen da gwamnatin ta Nijar ta yi. To amma wasu 'yan Nijar din kamar Malam Siraji Issa na kungiyar MOJEN, na zargin gwamnatin Janar Abdourahamane Tchiani da neman haddasa rikici tsakanin Nijar din da Najeriya ta hanyar wannan zargi.
Gwamnatin ta Nijar dai ta yi kira ga kasashen duniya da ma kungiyoyin kasa da kasa, kama daga kungiyar Tarayyar Turai EU da Majalisar Dinkin Duniya da sauran kasashen duniy masu neman zaman lafiya da su tashi su dauki matakin taka wa Faransa birki game da wannan aniya tata ta neman shinfida sabon mulkin mallaka. Kana ta yi kira ga 'yan kasa da su kasance cikin shirin ko-ta-kwana, su kuma bayar da hadin kansu ga mahukunta.