Alakar Shugaba Muhammadu Buhari da Sanata Bukola Saraki
October 2, 2015A karon farko cikin watanni uku tun bayan da aka zabe shi a matsayin shugaban majalisar dattawan Najeriya an ga shugaban majalisar na raha har da dariya shi da shugaban kasar Muhammadu Buhari, yanayin da a wattani ukun da ya yi yana jagorantar majalisar bayan hasashen zaman tankiya a tsakanin bangarorin biyu ba a taba gani ba.
Rikicin Shugabanci
Yadda Sanata Bukola Saraki ya dare kan mulkin shugabancin majalisar ya haifar da zaman tankiya a tsakanin majalisar dattawan da ma samar da bangarori biyu na Unity Forum da Like minds, inda ta kai ga kama hanyar baiwa hammata iska a tsakanin bangarorin biyu, kana zaben na Saraki bai yi wa jam'iyyarsa ta APC dadi ba. Wannan sauyi dai na zama alamar da ka iya samar da mafita a kasar.
Sanin cewa a lokutan baya dai an ruwaito cewa shugaban majalisar dattawan Najeriyar ya yi iyakar kokarin ganawa da shugaban Najeriya ba tare da samun nasara hakan ba, a yanzu da aka ga wannan sauyi ko wane tasiri zai yi ga yanayin gudanar da majalisar? Alhaji Isa Tafida Mafindi gogaggen dan siyasa ne a Najeriyar ya ce hakan na da matukar muhimmanci ga dorewar siyasar kasar.
Zaman tankiya a majalisun Najeriya
A majlisun dokokin da suka gabata dai zaman tankiya a tsakanin bangarori biyu na zartaswa da na majalisar dokokin Tarayyar Najeriyar ya kawo cikas ga gudanar da gwamnati musamman fanin yi wa talakawa aiki, abin da ya sanya nuna damuwa a kan halin da majalisar ta takwas ke ciki a yanzu, musamman a gwamnati APC da ita ce ta farko ta ‘yan adawa da ta kai ga madafan iko a kasar. Abin jira a ganin dai shi ne ko za'a ga canji da ma dorewar dangantakar a tsakanin sassan biyu, musamman sanin cewa shugaban majalisar dattawan na fuskantar shari'a a kotun da'ar ma'aikata bisa zargin kin bayyana kadarar da ya mallaka?