1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rudani na neman mamaye jam'iyar APC mai mulki

February 2, 2023

Kace-na-ce ya barke a tsakanin gwamnan Kaduna Nasiru El Rufa'i da ke zargin akwai zagon kasa daga bangaren Aso Rock da kuma fadar gwamnatin da ke fadin bata da zabin dan takara.

https://p.dw.com/p/4N24L
Muhammadu Buhari da Bola Ahmed Tinubu
Muhammadu Buhari da Bola Ahmed TinubuHoto: Official-State House Abuja Nigeria

Lokaci irin wannan dai a cikin al'ada, na zaman na hadin kai a cikin jam'iyyar APC da ke da fatan dorawa bisa mulki na kasar. To sai dai kuma ya zuwa yanzun rikicin na neman mamaye jam'iyyar APC mai mulki in da kawuna ke kara rabewa bisa yakin neman zabe na shugaban kasar.

Tuni dai dama aka rika kallon taku na gwamnatin kasar da alamun juyawa dan takara na jam'iyyar APC Bola Ahmed baya. To sai dai kuma kalaman gwamnan jihar Kaduna Nasir El Rufa'i dai sun dada tabbatar da zaman marina cikin APC da ke da fatan dorawa bisa mulki amma kuma ke zargin 'yan uwa da maitar gado.

Jam'iyyar APC nai mulki
Jam'iyyar APC nai mulkiHoto: Ubale Musa/DW

El Rufa'in dai bai boye rawar da ya ce wasu a cikin fadar gwamnatin kasa ke takawa da nufin tabbatar da tuntube na jam'iyyar da kila ma kare mulki na masu tsintsiyar dake fatan dorawa a gaba. Zargin kuma da ya bata ran jami'ai na gwamnatin kasar dake fadin ba wani maye a cikinsu.

Wannan gwamnati ta mai da hankali wajen tabbatar da karbabben zabe. Kuma mafi muhimmanci a cikin wannan tafiya na zaman shugaban kasa, ya kuma nuna aniyarsa ta tabbatar da ingantaccen zabe. Kuma ya nuna da kalamansa da kila ma aikinsa, cewar yayi imanin tabbatar da ingantaccen zabe. Abun kuma da yake nufin ba dan mowa a idanunsa. Kuma duk in da yaje yana maimaita haka. Ko a ranar juma'ar data gabata a yayin da ke yake Daura.

Saboda haka in akwai wani da yake zagon kasa ga wani dan takara to mu bamu san wannan ba. Koma ya take shirin kayawa a tsakanin fadar gwamnatin da masu tsintsiyar dai, kafin gwamnan na Kaduna dai shi kansa dan takara ya rika kaikaicewa yana bugu ga fadar da ya ke da tunanin bata shirin ta taimaka masa.

Nigeria l APC Ergebnis l Präsidentschaftskandidat
Buhari da Tinubu Hoto: Nigeria Prasidential Villa

Shi kansa kalaman gwamnan dai a fadar daya a cikin  kakakin yakin neman zaben na Tinubu  Mohammed Idris Malagwi  dai na tabbatar da dogo na hasashe na masu neman nasarar ta Jagaba. Koma ina ake shirin zuwa a cikin rikicin na masu tsintsiya dai, sannu a hankali fagen siyasar ta kasar na dada zafi da nuna alamun fadawa rudani yanzu.

Kuma a fadar Isyaku Ibrahim da ya dauki lokaci yana taka rawa ta siyasa, take take na gwamnatin na da babban burin rushe zaben da ke da tasiri ga makomar kasar.