Sabuwar Shugabar gwamnatin Jamus Angeller Merkel ta ziyarci Faransa da Belgium
November 23, 2005Kwana daya, bayan da yan majalisar dokokin Bundestag, su ka zabi Angeller Merkel ,a matsayin sabuwar shugabar gwammnatin Jamus, tunni ta fara aiki gadan gadan inda a sahiyar ta kai ziyara farko a kasar Fransa.
Angeler Merkell ta zabi Fransa a domin nuna wa hukumomin kasar mahimancin hadin kai tsakanin Fransa da Jamus, kasashe 2 dake sitiyarin tuka nahiyar turai baki daya.
Idan ba a manta ba a lokacin mulkin Geher Schröder, wannan kasashe sun zama tamkar dan juma da jan jummai a dandalin diplomatia na dunia.
A mafi yawan lokkata, shawarwarin su, da manufofin su kan zama iri daya, a kungiyyar gamayya turai da sauran huldodin kasa da kasa, a dandalin siyasdar dunia.
A ganawar ta da shugaba, Jacke Shirak, ya bayyana matukar burin ci gaba, da huldodin kut da kut, da ya kulla tare da tsofan shugaban gwamnatin Jamus Geher Schröder.
Haka zalika, sunyi masanyar ra´ayoyi a game da kungiyar gamayya turai, kamin kimanin kwanaki 20, na taron shuwagabanin kasashe membobin kungiyar.
Bayan kasar Fransa Merkel ta ziyarci kasar Brussels inda tag aan da shugabanhukumar zartaswa na kungiyxar EU Jose Manuel Barosso inda su ka tantanaa batutuwan da su ka shafi tafiyar da al´amuura a kungiyar.
A yayin da ta gana da sakataran kungiyar tsaro ta NATO dake Brusseles, Angeler Merkel ta bayyana burin ta, na karffafa huldodi tsakanin Jamus da Amurika.