Sace mutane don yin tsafi a Najeriya
January 27, 2016
Wannan aiki da matsafa ke yi dai yanzu haka na kokarin zama ruwan dare duba da yadda ya ke cigaba da faruwa a sassa daban-daban na Najeriya. Na baya-bayan nan dai shi ne wanda ya auku a birnin Zariya na jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya inda aka sace wani yaro kara tare da kwakule idanuwansu biyu a 'yan kwanakin da suka gabata. Wannan danyen aiki da ya sanya kungiyoyin da ke rajin kare hakkin bani Adama yin wani taro na manema labarai a Kaduna inda suka bukaci gwamnati da ta hanzarta wajen daukar dukkanin matakan da suka cancanta da zumar dakile cigaba da yn wannan mummunar dabi'a wanda suka ce tauye hakki ne bani Adama.
Mrs Madinate Shobaye da ke zaman sakatariyar kungiyar Lead of Children a Nigeria ta ce abin takaicin da suka ganewa idanunsu kwanakin da suka gabata a Nigeria sakamakon cirewa yaro idansa da aka yi ba zai musaltu ba duba da irin karfin da aka yi amfani da shi wajen cire idanun. Ita dai wannan kungiya ta danganta wannan aika-aika da aka yi da irin rashin tsaron da ake fuskanta a kasar.
To baya ga irin wannan tsari na danne mutum a cire masa ido don yi tsafi, wani sabon salo da aka fito da shi kuma shi ne satar mutane a masallatai musamman ma wanda ke da kankantar shekaru, wannan ne ma ya sanya kungiyar Jama'atul Nasrul Islam yin kira ga iyaye da suk taka-tsantsan da yaransu musamman ma dai wanda suka isa aike.