Rundunar tsaron Turai a yankin Sahel
July 6, 2021Ita dai wannan rundunar tsaro, za ta yi aikin sintiri a yankin magamar iyakoki uku na Jamhuriyar ta Nijar da Mali da Burkina Faso mai fama da hare-haren kungiyoyin 'yan ta'adda. Rahotanni sun nunar da cewa, Jamus ce za ta dauki nauyin kimanin kaso 90 cikin 100 na kudin kafa wannan runduna. Shugabar Hukumar Tarayyar Turan mai kula da harkokin tsaro a yankin na Sahel Antje Pittelkau ce dai, ta sanya hannu kan wannan yarjejeniya da hukumar 'yan dsanda ta Nijar, domin kafa rundunar tsaron ta Compagnie Mobile de controle des Frontieres wato CMCF a takaice, a yankin Tillaberi mai iyaka da Mali.
Karin Bayani: Bukatar sake lale a fannin tsaron Jamhuriyar Nijar
Laftanal Kanal Henry Gomez na kasar Faransa, na daga cikin shugabanni a hukumar ta EUCAP Sahel, ya yi karin haske kan yarjejeniya ta kunsa: "Bangarorinmu biyu sun cimma matsayar kafa rundunar tsaron kan iyaka ta CMCF wacce ta kunshi jami'an 'yan sanda 250, wadanda za a jibge a yankin Tera musamman a magamar iyakoki uku na Nijar da Mali da Burkina Faso da ke cike da hadari. Muna kyautata zaton jibge wannan runduna zai taimaka wajen bayar da kariya ga al'ummar yankin, wadanda yanzu haka suka kagu su ga an kafa ta. Shirin zai lashe kudi miliyan 10 na Euro domin daukar ma'aikata da samar musu da kayan aiki da kuma gina musu cibiyarsu nan da shekara guda."
Wannan dai ita ce rundunar sintirin kan iyaka ta uku da hukumar ta EUCAP Sahel ta kafa a Nijar, domin yaki da ta'addanci da masu aikata muggan ayyuka da fataucin miyagun kwayoyi da makamai da ma bakin haure, baya ga ta farko wacce aka kafa a kan iyakar Maradi da Najeriya da kuma ta tsakanin Konni da Najeriyar. Jamus ce dai ta dauki kimanin kaso 60 daga cikin 100, na kudin kafa wadannan rundunonin tsaro a kasar ta Nijar. Yanzu haka dai hukumomin kasar ta Nijar, sun bayyana bukatar samun goyon bayan kasashen na Turai da Amirka a nan gaba domin kafa karin wasu rundunonin sintirin kan iyakar kimanin guda 10 da nufin kula da illahirin kilomita dubu biyar da 800 na iyakokin kasar.