1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Antony Blinken zai gana da jagoran Falasdinawa Mahmoud Abbas

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
January 10, 2024

Mr Blinken da ke ziyararsa ta 4 a Gabas ta Tsakiya tun bayan fara rikicin, ya shaidawa manema labarai cewa Amurka za ta ci gaba da tallafa wa babbar aminiyarta Isra'ila

https://p.dw.com/p/4b2ub
Hoto: Kobi Gideon/GPO/Anadolu/picture alliance

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken zai gana da shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas, kan yadda tsarin jagorancin yankin Gaza zai kasance bayan kawar da Hamas.

Karin bayani:Sakataren harkokin wajen Amurka Blinken zai fara wata ziyarar aiki a Gabas ta Tsakiya

Mr Blinken da ke ziyararsa ta 4 a Gabas ta Tsakiya tun bayan fara rikicin, ya shaidawa manema labarai cewa Amurka za ta ci gaba da tallafa wa babbar aminiyarta Isra'ila, to amma ya bukace ta da ta kaucewa hallaka fararen hula.

Karin bayani:Blinken ya gana da shugaban Falasdinawa

Kamfanin dilancin labaran Faransa AFP ya rawaito cewa Blinken ya fara ganawa ne da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a Talatar nan birnin Tel-Aviv.