1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Blinken ya gana da shugaban Falasdinawa

November 6, 2023

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya ziyarci shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas a yankin gabar yamma da kogin Jordan da Isra'ila ta mamaye.

https://p.dw.com/p/4YRDO
Antony Blinken tare da Mahmud Abbas
Antony Blinken tare da Mahmud AbbasHoto: PPO/AFP

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya kai ziyarar ba-zata da gabar yammacin kogin Jordan, a daidai lokacin da Isra'ila ke ci gaba da luguden wuta a kan Zirin Gaza.

Babban jami'in diflomasiyyar Amurkar ya jaddada cewa Amurka za ta kai muhimman kayayyakin jinkai da ake matukar bukata a Gaza.

Antony Blinken ya kuma ce ba za a tilasta wa falasdinawa barin yankinsu da karfin tuwo ba.

Kakakin shugaban shugaban falasdinawa Abbas, ya shaida wa Blinken cewa akwai bukatar a tsagaita wuta ba tare da wani bata lokaci ba a Gaza.

Hukumar yankin falasdinu ce dai ke gudanar da gabar yammacin kogin Jordan, sai dai ba ta da iko da Zirin Gaza wanda kungiyar Hamas ke rike da shi tun cikin shekarar 2007.

Tuni ma dai Antony Blinken ya isa Turkiyya inda zai gana da Shugabab Racep Tayip Erdogan na kasar.