Antony Blinken na ziyarar ba zata a Ukraine
May 14, 2024Sakataren harkokin wajen Amurka na wata ziyarar ba zata a birnin Kiev a daidai lokacin da Rasha ke kara tsananta barin wutar da take yi a yakunan Arewa maso gabashin Ukraine.
Karin bayani: Amirka ta amince da bai wa Ukraine tallafin yaki
Karo na hudu kenan da babban jami'in diflomasiyyar ke kai ziyara a Ukraine bayan mamayar da Rasha ke yi wa makwabciyar kasar tun a cikin watan Febrairun 2022.
Manufar ziyara ita ce na kara jaddada wa Ukraine da ke fuskantar matsin lamba a fagen daga cikakken goyon bayan Amurka, tare da nuna adawa da kara fadada yakin da Rasha ke yi a yankunan Kharkiv, kamar yadda wani jami'in diflomasiyyar Amurka da ke tare da tawagar Antony Blinken ya shaida wa manema labarai.
Karin bayani: Amurka za ta bai wa Ukraine sabon tallafi
Ko a makon da ya gabata majalisar dokokin Amurka ta amince da karin kunshin tallafi ga gwamnatin Ukraine da ya kai dala biliyan 61, makonni bayan kai ruwa rana a gabanin ta kada kuri'ar amincewar.