Sakin 'yan jaridar Jamus a Iran
February 19, 2011Talla
Wata kotu a ƙasar Iran ta ba da izini a saki wasu Jamusawa 'yan jarida biyu da aka zarga da leƙen asirin ƙasar. Jamusawan waɗanda suka haɗa da Marcus Hellwig da Jens Koch tun a watan Oktoban bara ake tsare da su, inda alƙalin kotun ya yanke musu hukuncin ɗaurin watanni 20, amma da zaɓin biyan tara ta euro dubu 35, bisa wani abin da alƙalin ya ce saɓa wa ka'idar tsaron ƙasar ta Iran ne. 'Yan jaridar an same ne su da laifin shiga ƙasar ta Iran ta barauaniyar hanya, bayan da suka nemi visa ta yawon shaƙatawa, amma aka same su suna hira da ɗan Sakineh Ashtian da aka yanke wa hukuncin rajamu bisa laifin zina.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Halima Balaraba Abbas