Harin kunar bakin wake yayin sallar Idi a Damaturu
July 17, 2015Wadannan bama-bamai dai sun tashi ne a dai-dai lokacin da jama'a suka fara taruwa don halartar Sallar Idi. Kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Yobe Markus Danladi ya tabbatar wa da manema labarai cewa mutane 13 ne suka mutu wasu 15 kuma suka jikkata sanadiyyar harin da ya bayyana da na kunar bakin wake.
Kalubalen sabuwar rundunar tsaro
A cewar kwamishinan ‘yan sandan wasu yara mata ne guda biyu suka nufi kai wannan tagwayen hare-hare da ya kare a kan wadanda suke binciken masu zuwa Masallacin domin yin Sallah. Tuni dai aka garzaya da wadanda suka samu raunuka dama gawarwakin wadanda suka rasu zuwa babban asibitin da ke garin Damaturun. An kai wadannan hare-haren ne dai a dai-dai lokacin da sabon babban hafsan sojojin Najeriyar ya je Damaturun domin yin Sallar Idi da dakarunsa. Tuni dai rundunar sojojin ta Najeriya ta fitar da wata sanarwa da ke nuni da cewa babban hafsan sojoji da kuma gwamnan Yobe sun jajanta wa wadanda abin ya rutsa da su inda kuma suka bukace su da su zama masu taka tsatsan da lamuran tsaro.
Bukukuwan Sallah cikin fargaba
Wannan tagwayen hare-hare da ma wanda ya faru a ranar Alhamis din da ta gabata wato jajiberin Sallar a babbar kasuwar garin Gombe sun sanya gudanar da bukukuwan Sallar a shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya cikin fargaba da tashin hankali inda wasu jama'a da dama ba su samu zuwa Sallar Idin ba. Sai dai duk da haka an yi Sallar Idin lami lafiya a sauran jihohin shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriyar, koda ya ke ‘yan gudun hijira sun koka da rashin samun tallafi da kulawar da ta kamata daga bangaren hukukumomi kuma mafiya yawa sun yi Sallar ne cikin kunci da rashin abin sawa a bakin salati.