1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Sama da mutane 5,000 sun mutu a Gaza tun bayan fara rikici

Mouhamadou Awal Balarabe
October 23, 2023

Sabon rahoton da ma'aikatar lafiya ta Hamas ta fitar ta nunar da cewar akalla mutane 5,087 sun mutu tun bayan fara luguden wuta da Isra'ila ke yi a zirin Gaza, yayin da ayarin kayan agaji na uku ya shiga zirin daga Rafah

https://p.dw.com/p/4XuB7
Mace-mace na karuwa a zirin Gaza sakamakon rikici tsakanin Isra'ila da Hamas
Mace-mace na karuwa a zirin Gaza sakamakon rikici tsakanin Isra'ila da HamasHoto: MAHMUD HAMS/AFP/Getty Images

Ayarin kayan agaji na uku ya shiga zirin Gaza daga Rafah da kan iyakar Masar da yankin na Falasdinawa, a daidai lokacin da Isra'ila ke ci gaba da luguden wuta don karya lagon Hamas da wasu kasashen Yamma ke dangantawa da kungiyar 'yan ta'adda.  Wani jami'in kungiyar ba da agaji ta Red Crescent na Masar ya shaida wa AFP cewa motoci 34 ne suka tsallaka Rafah cikin kwanaki biyu, yayin da  Majalisar Dinkin Duniya ke kiran da a shigar da akalla manyan motoci 100 a kowace rana ga 'yan Gaza miliyan 2.4.

Karin bayani: Isra'ila ta yadda da fara kai agaji Gaza

Shi ma babban jami'in kula da harkokin waje na Kungiyar Tarayyar Turai Josep Borrell ya goyi bayan tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas don ba da damar kai kayan agaji zuwa zirin Gaza. Mista Borell ya shaida wa manema labarai a Luxembourg cewa, babban abin da ya fi daukar hankali a halin yanzu shi ne isar da kayayyakin jin kai zuwa zirin Gaza.

Karin bayani: Fargabar kisan kiyashi a yankin Zirin Gaza

Wani sabon rahoton da ma'aikatar lafiya ta Hamas ta fitar ta nunar da cewar akalla mutane 5,087 ne ne suka mutu tun bayan fara luguden wuta da Isra'ila ke yi a zirin Gaza. Sannan ta  kara da cewa akalla mutane 15,273 ne suka samu raunuka ya zuwa rana ta 17 na rikicin da Isra'ila ke yi da Hamas.