Najeriya: Samame a kasuwannin 'yan canji
February 21, 2024Wannan dai na zuwa ne, a daidai lokacin da darajar kudin kasar wato Naira ke kara faduwa wanwar. Hatsaniya dai ta kaure a lokacin da jami'an tsaron Najeriyar a suka hadar da 'yan sanda da ma wadanda ke a farin kaya, suka afkawa kasuwar ta 'yan canji a Abuja fadar gwamnatin kasar. Wannan matsalar dai ta janyo harbe-harbe a iska, domin tsorata 'yan kasuwar da mafi yawansu suka arce domin gujewa kamen da jami'an tsaron ke yi. Mummunan faduwar da darajar takardar kudin Najeriyar ta Naira ke yi in aka kwatanta da sauran takardun kudi na kasashen waje musamman dallar Amurka, inda ta kai Naira 1900 kuma take ci gaba da kara karyewa na dada tayar da hankali sosai. Wannan mataslar ta janyo hauhawar kayan masarufi, inda kusan kowane dan kasuwa ke auna farashinsa da nawa ake sayar da dallar. Batun farashin kudadden kasashen waje a Najeriyar musamman dalar Amurka, ya jefa rayuwar al'ummar kasar cikin mawuyacin hali na hauhawar farashin kayayyaki da ya kai kaso 29 cikin 100 wanda shi ne mafi muni a shekaru 17 da suka gabata.