Matsalar samun jini a Ghana
June 18, 2024A Ghana masu ruwa da tsaki sun fara kokawa da neman ganin karshen biyan kudi kamin samun jini a asibitoci kamin a dorawa majinyaci kwalba daya na jini a duk yadda yanayi ya kama, ko ga mai juna biyu a wajen haihuwa, masu ciwon sikila, masu matsalar koda a lokuttan haddura da duk yanayin bukatar jinin gaugawa. Inda masu ruwa da tsakin ke neman sauyi tare da hukumar bada inshoran kiwon lafiya a kasar.
Karin Bayani: Ghana ta samu ci gaba ta fuskar arzikin zinare
Duk da muhimmancin tabbataciyar hanyar samarda jini dan wanzar da kiwon lafiya a tsanake, a Ghana dangata da asibitin, kowane kwalba daya na jini na sayuwa ne akan $18 zuwa $34, ba tareda kayyadaden firashe ba. Ga kowace mai juna biyu, doka ce ma ta yi tanadin jini au ta biya kudin jinin ko kuwa wani nata ya ba da kamin ranar haihuwa. Akwai damuwa a bayanan alkalluma a baya-bayan nan da ke nunin jan kafar jama'a masu ba da jinin su kyauta. A shekarar 2021, an samu kyautan jinin 173, 938 dake yin kaso 26% daga jama'a, akasin kaso 25.3% na adadin 179,765 a shekarar 2022 wanda daga 'yan uwa ne na masu jiyya. Ana dai kara kira ga masu bada jini kyauta wanda a yanzu yayi karanci sosai. Wanda cibiyar bada jini ta kasa ta iya samarda adadin wanda ya zarce 50,000 da kalilan a shekarar 2023.